Litinin, Mayu 02, 2016 Karfe 13:33

  Labarai / Afirka

  Gwamnan Jihar Kaduna Patrick Yakowa Ya Rasu

  Marigaryi Gwamnan jihar Kaduna Patrick Yakowa a cikin shudiyar riga
  Marigaryi Gwamnan jihar Kaduna Patrick Yakowa a cikin shudiyar riga
  Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da rasuwar gwamnan jihar Kaduna Patrick Yakowa da kuma tsohon mai baiwa shugaban kasa shawarwari kan harkokin tsaro janar Owoye Azazi, sakamakon hadarin jirgin helicofta da ya auku a kauyen Nambe na jihar Bayelsa inda suka je domin halartar jana’izar mahaifin Oronto Dauglas daya daga cikin mukarraban shugaba Goodluck Jonathan.

  A cikin hirarsa da Sashen Hausa Rev Joseph Hayeb daya daga cikin masu ba  marigayi Patrick Yakowa shawarwari kan harkokin addini ya bayyana cewa, gwamna Yakowa ya tashi daga Kaduna zuwa Patakwal a wani jirgi dabam kafin daga wurin suka shiga karamin jirgi zuwa Nambe inda aka yi jan’izar.

  Bayan jana’izar ne janar Azazi  ya gayyaci Mr. Yakowa da dogarinsa su shiga  jirgi mai saukar angulu na mayakan ruwa da zai koma a ciki kasancewa akwai sauran kujerun mutum biyu. Tashinsu ke da wuya kan hanyarsu zuwa tashar jirgin sama ta Patakwal dake tazarar tafiyar kimanin minti 18 hadarin ya auku, nan da nan bayan kuccewar jirgin ya kama da wuta abinda ya sa aka gaza kai dauki.

  Fadar shugaban kasa ta Najeriya ta bayyana takaicin rashin. Ta kuma bayyana sunayen sauran wadanda suka rasa rayukansu a hadarin da suka hada da dogarin janar Azazi Mohammed Kamal, da dogarin gwamna Patrick Yakowa Dauda Tsoho da kuma matukan jirgin Murtala Mohammed Daba da Lt. Adeyemi O. Sowole

  Shugaba Goodluck Jonathan ya aika ga sakon ta’aziya ga dangi da abokai da gwamnatoci da kuma illahirin al’ummar jihohin Kaduna da Bayelsa ya kuma bada umarnin bincika masababin hadarin.

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shrin Safe
   Minti 30

   Shrin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye