Jumma’a, Afrilu 29, 2016 Karfe 16:53

  Labarai / Kiwon Lafiya

  Hukumar lafiya ta Duniya ta amince a ba masu lafiya maganin cutar kanjamau

  Wata mata da yaro masu cutar kanjamauWata mata da yaro masu cutar kanjamau
  x
  Wata mata da yaro masu cutar kanjamau
  Wata mata da yaro masu cutar kanjamau
  Hukumar lafiya ta duniya ta goyi bayan ba wadanda suke gudun kamuwa da cutar kanjamau maganin rashin kaifin cutar. Hukumar ta kuma shawarci kasashe masu karfin arziki su kaddamar da tsarin gwada shirin domin a kara fahimtar amfanin shirin.

  Hukumar ta bada wannan shawarar ne bayan masu sa ido kan ingancin magunguna na Amurka suka amince da maganin  da rage kafin cutar kanjamau da ake kira Truvada, ga mutanen da basu dauke da cutar amma yana yiwuwa su yi jima’I da wadanda ke dauke da cutar kanjamau. Ana kiran wannan tsarin da turanci “pre-exposure prophylaxis”, ko PrEP a takaice.

  Ana amfani da maganin  Truvada ya kunchi sauran magungunan da ake amfani da su wajen rage kaifin cutar kanjamau a jinyar wadanda ke daukar da kwayar cutar HIV dake haddasa cutar kanjamau. Maganin da kudin amfani da shi ya kai dala dubu 14 a shekara a Amurka, shine magani rigakafin kamuwa da cutar na farko da aka amince da shi.

  Hukumar lafiya ta duniya tana karfafa kasashen da suke sha’war amfani da tsarin rigakafi na PrEP su fara kaddamar da shirin wayarwa da ma’aikatan jinya kai dangane da amfanin shirin kafin aiwatar da shi. Hukumar ta kuma kafafa bada magungunan kanjamau ga wadanda suke fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

  Kawo yanzu  sama da kasashe 112 da suka hada da kasashen da suka fi fama da cutar HIV kamar Indiya da Thailand da kuma Afrika ta Kudu, suna samun magunguna masu saukin kudi dake kama da maganin Truvada,da kudinshi mai wuce dala 8 ba a wata, Karkashin wani shiri na musamman na wadansu kamfanonin magani na kasar Indiya.
  An gudanar da binciken na PrEP ne tare da tallafi daga gidau niyar Bill da Milinda Gates a yunkurin magance yada kwayar cutar kanjamau.

  Watakila Za A So…

  Sauti Boko Haram Na Shigar Da Makamansu Najeriya Ta Boyayyun Hanyoyi

  Tsohon hafsan rundunar sojan saman Najeriya, Aliko El-Rashid Harun, wanda kwararre ne kan sha’anin tsaro yace akan shigo da makamai ga yan Boko Haram cikin Najeriya ta kan iyakokin kasar, wanda ke da yawan gaske kuma ba a saka musu idanu. Karin Bayani

  Sauti Ra’ayoyin Yan Jihar Kaduna Game Da Wasu Dokoki A Jihar

  Wasu daga cikin yan jihar Kaduna da shugabannin al’umma na ci gaba da korafe korafe game da wasu daga cikin dokokin da gwamna mallam Nasiru El-Rufa’in jihar Kaduna yakai gaban Majalisa. Karin Bayani

  Sauti An Kai Hari A Garin Egrak A Jamhuriyar Nijar

  Wandansu mutane da ba a san ko suwaye ba sun kai hari a yammacin jiya, a wani kauye da ake kira Egrak, dake cikin jihar Tawa a kasar jamhuriyar NIjar. Karin Bayani

  Harin Aleppo dake kasar Syria ya batawa sakataren harkokin wajen Amurka rai

  Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace ran shi ya baci kwarai saboda harin jirgin saman yaki da aka kai kan asibitin yara dake birnin Aleppo kasar Syria. Karin Bayani

  Majalisar Dinkin Duniya ta dage takunkumin da ta kakabawa Ivory Coast

  Jiya Alhamis kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ya dage takunkumin shekaru goma sha biyu na hana sayarwa kasar Ivory Coast makamai Karin Bayani

  Sauti Shugaban hukumar NYSC ya kai tallafi sansanin 'yan gudun hijira a Adamawa

  Shugaban hukumar kula da masu yiwa kasa hidima Birgediya Janar Sule Zakari Kazaure ya ce bana hukumar zata aika matasa masu yi wa kasa hidima zuwa yankuna da sojojin Najeriya suka kwato daga hanu Boko Haram a karon farko cikin shekaru hudu. Karin Bayani

  Sauti

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye