Jumma’a, Maris 27, 2015 Karfe 00:43

Sauran Duniya

Koriya Ta Arewa Ta Harba Roka Mai Cin Dogon Zango

Tashar Talabijin ta Koriya Ta Arewa ta nuna ana harba roka
Tashar Talabijin ta Koriya Ta Arewa ta nuna ana harba roka
Koriya Ta Arewa ta ce ta samu nasarar harba roka mai cin dogon zango, tare da kai wani tauraron dan Adam da zai rika kewaya duniya, a bayan da ta sanya kafa ta shure gargadin da Majalisar Dinkin Duniya da kuma makwabta suka yi mata na kada ta yi hakan.

Kamfanin dillancin labaran gwamnati na kasar yace wannan roka samfurin Unha-3 ta samu nasarar cirawa yau laraba daga cibiyar binciken sararin samaniya ta Sohae, kuma tauraron dan Adam da take goye da shi ya samu nasarar kaiwa inda zai tsaya yana kewaya duniya kamar yadda aka shirya.

Jami’an tsaro na kasashen Kasashen Ta Kudu da Japan sun tabbatar da cewa dukkan gabobi guda uku na wannan roka da alamun sun yi aiki zuwa ga wuraren da zasu balle daga jikin uwar rokar kamar yadda Koriya Ta Arewa  ta fada zasu yi tun da fari. Amma kuma ba zasu iya gaskata ko tauraron dan Adam din da take dauke da shi ya kai inda zai rika zagaya duniya ba.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce ta lura da harba rokar, kuma tana nazarin lamarin.

Jami’an diflomasiyya sun ce a yau laraba Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai gana bisa rokon Amurka da Japan, domin tattauna harba rokar da Koriya Ta Arewa ta yi. Koriya Ta Kudu da Japan kuma sun kira wani zaman gaggawa na manyan jami’an tsaronsu kan wannan batun.

Kafin harba wannan roka, masu fashin baki sun bayyana ta a zaman makami mai linzamin da aka boye kamanninta, matakin da ya saba ma dokokin kasa da kasa.
Koriya Ta Arewa ta lashi takobin ci gaba da harba rokar kamar yadda ta shirya duk da rashin kyawun yanayi da kuma tangardar injin da ta yi ta samu.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti