Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LIBYA: Hukumomi Sun Fi Kutuntawa Mutane


Mayakan sa kai suna neman 'yan ISIS a Libya
Mayakan sa kai suna neman 'yan ISIS a Libya

Kungiyar kare hakkokin bil adama ta duniya ta Human Rights Watch ta zargi kusoshin gwamnatin Libya da cewa sun fi maida hankali wajen kuntatawa mutanen dake tsare a hannunsu da tilasta musu daukan laifukkan da basu aikata ba da kuma toshe musu hanyoyin neman hakkokinsu, maimakon samar musu taimakon magungunna.

A yau Laraba ne jami’an cibiyar kare hakkoki bil,adama din suka fito da rahoton nasu bayan ziyarar gani-da-ido da suka kai a wasu wurare ukku da ake tsare da sojan Libya tareda jami’an ma’aikatar harakokin cikin gida ke tsare da mutanen a gabashin kasar ta Libya.

Cibiyar ta H-R-W tace a wadanan wuraren dake Benghazi da al-Bayda, akwai mutane kamar 450 da ake tsare da su wadanda kuma akalla rabinsu suka ce an gana musu azaba, yayinda dukkansu suka ce ana hana su ganin lauyoyin da zasu iya kare su, ko ma a kaisu a gaban alkali, kai, ko ma a tuhumce su ba’a yi ba.

VOA60 Afirka: Kotun Koli A Libya ta Haramta Majalisar Dokokin Kasar, LIbya, Nuwamba 06, 2014
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:59 0:00

Mulkin kasar ta Libya dai yanzu an raba shibiyu a tsakanin gwamnatin dake da amincewar kasashen duniya wacce mazauninta ke a Tobruk da kuma wacce mayakan sa-kai suka kafa, mai hedkwata a Tripoli, babban birnin kasar.

Mutanen dake tsare a Libya
Mutanen dake tsare a Libya

XS
SM
MD
LG