Talata, Satumba 02, 2014 Karfe 23:45

Kiwon Lafiya

Matasa dubu dari bakwai suke dauke da kwayar cutar HIV a Najeriya

Wani darektan majalisan dinkin duniya yace matasa dubu dari bakwai ne suke dauke da kwayar cutar kanjamau a Najeriya.

Wadansu matasa suna hira
Wadansu matasa suna hira
Kahli Abdu

Darektan cibiyar yaki da cutar kanjamau na Majalisar Dinkin Duniya Micheal Sidibe ya bayyana cewa, kimanin matasa dubu dari bakwai ne suke dauke da kwayar cutar kanjamau a Najeriya.

Darektan ya bayyana haka ne a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Bisa ga cewarshi, kimanin daya cikin biyar na wadanda ke dauke da cutar kanjamau a Najeriya matasa ne tsakanin shekara 15 zuwa 32.

Ya kuma bayyana cewa, kashi 24% na matasan ne kawai suka san matakan da ya kamata su dauka na kare kansu daga daukar cutar, da kuma yada ta. Mr Sidibe ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta hanzarta kafa dokar hana nunawa masu fama da cutar wariya.

Bisa ga cewarshi, wadanda ke dauke da cutar, sun yi wahala sakamakon wariya da ake nuna mana fiye da cutar da suke dauke da ita.

An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: ABDULLAHI HARUNA
01.08.2012 14:26
ALLAH YASADAI GABNATIN NAJERIYA TADAUKI SHAWAR WARIN DAZA ABATA AMIN

Rediyo/Sauti

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +1-202-619-0548 ko kuma +1-202-619-0551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +1-202-205-9942.
 

Audio Shirin Safe        MP3

Audio Shirin Rana       MP3

Audio Shirin Dare       MP3

Audio Mu Tattauna       MP3