Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nazifi Asnanic Zai Fito da Shu'uma


Shahararren mawakin Hausa, Nazifi Abdulsalami Yusuf, "Nazifi Asnanic"
Shahararren mawakin Hausa, Nazifi Abdulsalami Yusuf, "Nazifi Asnanic"

Nazifi Abdulsalami Yusuf, wanda aka fi sani da suna Nazifi Asnanic, ya dauki wani sabon fim na Hausa mai suna Shu'uma, kuma ya yi magana a kai

Duk da cewa an fi saninsa da waka, Nazifi Abdulsalami Yusuf, ko Nazifi Asnanic kamar yadda aka fi saninsa, yana taka rawa sosai a harkar fina-finan Hausa.

A tattaunawar da yayi da filin "A Bari Ya Huce..." shahararren mawakin yace babban gurin irin wadannan fina-finai shi ne aikewa da sako mai ma'ana, kuma mai amfani ga jama'a.

Makonni kadan da suka shige, an dauki sabon fim na Asnanic mai suna Shu'uma, fim din da ya kunshi wata sabuwar jaruma da kuma sanannu kamar su Jamila Umar Nagudu, mawaki Yakubu Mohammed, Lawal Kumurci da wasunsu.

A saurari bayanin da Nazifi Asnanic yayi kan wannan sabon fim na Shu'uma a kasa, kuma za a iya saurara cikin shirin "A Bari Ya Huce..." na asabar 27 Afrilu 2013.

Nazifi Asnanic Yana Magana Kan Shu'uma - 5:54
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:54 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG