Jumma’a, Afrilu 29, 2016 Karfe 13:03

  Labarai / Sauran Duniya

  Mr. Obama Da Romney Sun Kammala Yakin Neman Zaben Bana.

  A jajiberen babban zabe a nan Amurka, shugaba Barack Obama na Amurka da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican dake kalubalantarsa, Mitt Romney, sun yi yakin neman zabe na karshe a muhimman jihohin da sune zasu iya shata wanda zai lashe wannan zabe na yau talata, wanda har yanzu babu wanda yayi ma wani fintinkau a cikinsu.

  A Jihar Wisconsin, shugaba Obama ya zargi Mr. Romney da kokarin yin ado ma munanan manufofin da ‘yan Republican suka aiwatar a can baya, yana mai cewa kasar nan ba zata samu nasara ba har sai ta bunkasa al’ummar dake tsaka tsaki.

  Zamu ci gaba da gwagwarmayarmu a saboda mun san Amurka a koda yaushe tana bunkasa. Muna samun gawurta a duk lokacin da aka ba kowa dama, a duk lokacin da kowa ya dafa daidai wa daida, kuma a duk lokacin da kowa ke aiki da ka’idoji iri daya. Abinda muka yi imani ke nan. Wannan shi yasa kuka zabe ni a 2008, kuma wannan shi ne dalilin da yasa nake neman wa’adi na biyu a matsayin shugaban Amurka.

  A wajen wani gangamin da yayi da sanyin safiyar jiya a Jihar Florida, Mr. Romney ya fadawa magoya bayansa cewa shugaban dan jam’iyyar Democrat, ya kasa cika alkawuran da yayi har ya ci zaben 2008.

  Shugaban nan yayi alkawarin kawo canje-canje masu yawa, amma ai ba iya jawabi ne canji ba. Ana auna canji ne ta hanyar nasarorin da mutum zai gani a kasa. Shekaru hudu da suka shige, Obama yayi alkawura da yawa lokacin da yake takara, amma kuma kash, har yanzu ya kasa cimma su.
  Dan takarar shugabancin Amurka Mitt Romney yake hanu da shugaba Barack Obama.Dan takarar shugabancin Amurka Mitt Romney yake hanu da shugaba Barack Obama.
  x
  Dan takarar shugabancin Amurka Mitt Romney yake hanu da shugaba Barack Obama.
  Dan takarar shugabancin Amurka Mitt Romney yake hanu da shugaba Barack Obama.

  Masu fashin bakin siyasa a nan Amurka suka ce daga cikin jihohi guda hamsin na Amurka, ‘yan kalilan ne kawai zasu iya fayyace wanda zai ci zaben na yau talata, a saboda akasarinsu an riga an san ko dai shugaba Obama ko Mr. Romney ne zasu lashe su. ‘Yan jihohin da har yanzu ba a san wanda zai lashe su ba, sune ake yakin neman zabe kansu gadan gadan. Zaben shugaban kasa na Amurka, ba wai ana yinsa ne ta kirga illahirin kuri’un da aka kada domin ganin mai rinjaye ba, ana yinsa ne bisa tsarin zaben wakilai ko mazaba wadanda sune a zahiri zasu zabi shugaban kasa. Yawan wakilai ko mazaba na kowace jiha, ya danganci yawan jama’arta idan an kwatanta da sauran jihohin kasa.

  A bayan gangamin da yayi a Wisconsin, shugaba Obama ya yada zango a Jihar Ohio, kafin ya zarce zuwa Jihar Iowa, inda a yanzu haka yake gudanar da yakin neman zabensa na karshe. Mr. Romney ya yada zango a Ohio da Jihar Virginia, sannan ya zarce zuwa Jihar New Hampshire.

  Miliyoyin jama’a a kasar nan dai sun riga sun kada kuri’unsu karkashin dokokin jefa kuri’a da wuri a wasu jihohi. Amma mafi yawan masu jefa kuri’a yau ne zasu doshi rumfunan zabe da za a kakkafa a makarantu da gidajen ‘yan kwana-kwana da coci-coci.

  Kuri’un neman ra’ayoyin jama’a dabam-dabam sun nuna ‘yan takarar biyu su na kunnen doki a kasa. Amma a kuri’un neman ra’ayoyin masu jefa kuri’a a jihohi guda 9 wadanda sune zasu tantance wanda zai lashe wannan zabe, sun nuna shugaba Obama yana kan gaba a akasarinsu, amma da ‘yar rata kadan. Romney yana kan gaba a cikin jiha kwaya daya tak ne daga cikin wadannan jihohi, watau a Jihar Florida.

  Watakila Za A So…

  Harin Aleppo dake kasar Syria ya batawa sakataren harkokin wajen Amurka rai

  Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace ran shi ya baci kwarai saboda harin jirgin saman yaki da aka kai kan asibitin yara dake birnin Aleppo kasar Syria. Karin Bayani

  Majalisar Dinkin Duniya ta dage takunkumin da ta kakabawa Ivory Coast

  Jiya Alhamis kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ya dage takunkumin shekaru goma sha biyu na hana sayarwa kasar Ivory Coast makamai Karin Bayani

  Sauti Shugaban hukumar NYSC ya kai tallafi sansanin 'yan gudun hijira a Adamawa

  Shugaban hukumar kula da masu yiwa kasa hidima Birgediya Janar Sule Zakari Kazaure ya ce bana hukumar zata aika matasa masu yi wa kasa hidima zuwa yankuna da sojojin Najeriya suka kwato daga hanu Boko Haram a karon farko cikin shekaru hudu. Karin Bayani

  Sauti An jaddada mahimmancin koyon yin anfani da naurorin fasahar zamani

  A yayinda ake gudanar da bikin ranar mata a Bauchi an jaddada mahimmancin koyon yin anfani da narorin fasahar zamani domin ko karatun boko yanzu baya tafiya daidai idan ba'a anfani da naurorin ana shiga yanar gizo domin tara bayanai Karin Bayani

  Sauti Gwamnatin Nijar da malaman makarantun boko sun cimma daidaito

  Biyo bayan daidaiton da gwamnatin Nijar da kawancen kungiyar malaman makarantun boko suka cimma sun fitar da sanarwar bai daya inda malaman suka fasa fantsamawa cikin wani yajin aik Karin Bayani

  Sauti Najeriya da Faransa sun cimma yarjejeniyar yaki da ta'adanci

  Ministocin tsaron Najeriya da na Faransa sun kwashe kwanaki biyu suna ganawa akan hanyoyin dakile ta'adanci dake kawo tashin tashina a jihohin arewa maso gabashin Najeriya dake yaduwa zuwa kasashen yankin tafkin Chadi Karin Bayani

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye