Litinin, Agusta 03, 2015 Karfe 03:35

Labarai / Sauran Duniya

Rundunar 'yan tawayen Siriya ta sanar da maida shelkwatarta cikin kasar

Wani mayakin rundunar Free Syria yana shirin harba bindigaWani mayakin rundunar Free Syria yana shirin harba bindiga
x
Wani mayakin rundunar Free Syria yana shirin harba bindiga
Wani mayakin rundunar Free Syria yana shirin harba bindiga
Dakarun gwamnati da na ‘yan hamayya sun gwabza kazamin fada a duk fadin Siriya yau asabar, yayinda rundunar ‘yan tawaye ta Free Syrian Army ta sanar da cewa, zata maida cibiyar gudanar da ayyukanta daga Turkiya zuwa Siriya.

‘Yan gwaggwarmayar hamayya sun ce a kalla mutane 25 aka kashe a harin da dakarun tsaro suka kai wadansu wurare. Sun ce tashin hankali mafi muni ya faru ne a yankin Aleppo inda dakaru suka kai hare hare suna kokarin tarwatsa ‘yan tawaye daga wuraren da suke da karfi.

A halin da ake ciki kuma, dakarun rundunar mayakan Siriya-Free Syrian Army, da ta kunshi galibi sojojin da suka balle, ta fitar da wani hoton bidiyo dake cewa, zata maida cibiyar gudanar da ayyukanta zuwa wani bangaren kasar Siriya da aka “yanto”.

A cikin hoton bidiyon da aka nuna a tashar labarai ta al-jazeera, kanar Riad al-Assad na rundunar FSA yace kungiyar tana kyautata zaton kai farmaki a Damascus.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti