Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sha da fataucin miyagun kwayoyi na addabar kasashe masu tasowa


Miyagun kwayoyi da aka kama ana konesu
Miyagun kwayoyi da aka kama ana konesu

Sha da fataucin miyagun kwayoyi na cikin mayan kalubale dake addabar kasashe masu tasowa musamman wajen kawo koma baya ga tattalin arziki da dakushe kuzarin matasa maza da mata.

'Yan Najeriya masu safarar miyagun kwayoyi akan kamasu a yanke masu hukuncin kisa a wasu kasashen duniya.

Kasashe irin su Sin, Malaysia, Singapore da Saudiya sun sha yiwa 'yan Najeriya hukuncin kisa sau tari kuma wasu a yi masu daurin rai da rai.

Yara matasa sukan mayarda wasu abubuwa kayan maye kamar shekan fetur, solisho, kashin kadangare, yayinda wasu mata kuma ke shan benelin na maganin mura don samun marisa koko dogon barci.

Malama Halima Baba Ahmed mai kemfen din kangarewar matasa ta yi karin bayani kan illar miyagun kwayoyi. Masu shan kwalba goma na maganin da ya kamata ya sha cikin kwanaki biyar ya jima kwakwalwarsa. Wanda kuma ya sha maganin da anfaninshi ya kare tamkar ya kashe kansa da kansa ke nan. Yana iya haukacewa gaba daya.

Shan magani ba tare da izinin likita ba nada nashi illar. Usman Funtuwa, jami'in kiwon lafiya yace maganin da ka ba kanka tana yiwuwa jikinka baya son maganin. Idan ka sha maimakon ya yi maka magani sai ya yi wata illar ta daban. Haka ma yiwa kai allura rigima ce da ka iya kaiga wani mugun lahani.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG