Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Chibok, Babi na 2: Shin Ina Aka kwana Kan Batun Daliban Chibok?


Monica Stover uwar daya daga cikin yara mata fiye da 200 da aka sace a garin Chibok ke nan a taron manema labarai akan yaran da aka yi a Legas 5 ga watan Yuni, 2014.
Monica Stover uwar daya daga cikin yara mata fiye da 200 da aka sace a garin Chibok ke nan a taron manema labarai akan yaran da aka yi a Legas 5 ga watan Yuni, 2014.

An yi zanga-zanga a wurare da yawa wadanda suka hada da birnin tarayya Abuja, Kano, sudan.

Uwargidan gwamnan jihar Borno Nana Shettima ta kira wani taron gaggawan bisa ga labarin da aka samu cewa, an sace daliban makarantar sakandaren Chibok. Uwargidan gwamnan ta fada ma wadanda suka halarta cewa wasu ‘yan bindiga sun sace dalibai.

An sami rahotanni dayawa cewa ‘yan bindigar sun kai Daliban wurare dabam-da-dabam a jihar Borno. Iyayen daliban sun shaida cewa bamu sami wani bayani ba daga Jami’ai sai dai jita-jita akan inda ‘ya’yansu suke amma dai an fi kyautata zaton sun kaisu dajin Sambisa a lokacin.

Ranar talatin ga wata, mutane maza da mata sun yi zanga–zanga a gaban Majalisar tarayya dake Abuja don nuna rashin amincewarsu da abin daya faru kuma suna rokon gwamnati da ta dauki matakan ceto daliban na Chibok. Wasu daga cikin iyayen sun koka da halin da ‘ya’yansu ke ciki, ma’ana, cin su da shansu, makwancinsu, da irin mahallin da suke.

Majalisar wakilai ta yi Allah wadai da abinda ya faru ta kuma bukaci shugaban rundunar sojoji da ya gurfana a gabanta ba tare da bata lokaci ba a ta bakin senata Zainab Kure ‘yar majalisar dattawa.

An yi zanga-zanga a wurare da yawa wadanda suka hada da Kano, da sauran jihohi akan sace daliban. Ranar biyu ga watan Mayu, dalibai a Sudan da suka hada da ‘yan Najeriya, Sudan da Misira su ma ba a barsu a baya ba wajen zanga-zangar. Ranar uku ga watan mayu wasu daga cikin wakilan majalisar dattawan Amurka suma sukayi Allah wadai da abinda ya faru.

Wasu daga cikin daliban da Allah ya basu ikon kubuta, sun bada labari abinda ya faru. Daya daga cikin su tace “ta gwammace ta mutu a ga gawarta da ta shiga rayuwar da bata san makomarta ba".

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG