Lahadi, Maris 29, 2015 Karfe 04:07

Sauran Duniya

Shugaba Assad Ya Lashi Takobin Murkushe 'Yan Ta'adda

Shugaban na Sham ya lashi takobin raba kasar da 'yan ta'adda yayin da dakarunsa ke ci gaba da gwabzawa da 'yan tawaye a Aleppo da Damascus

Shugaba Bashar al-Assad na kasar Sham, wanda ya lashi takobin kawar da abinda ya kira 'yan ta'adda daga kasarShugaba Bashar al-Assad na kasar Sham, wanda ya lashi takobin kawar da abinda ya kira 'yan ta'adda daga kasar
x
Shugaba Bashar al-Assad na kasar Sham, wanda ya lashi takobin kawar da abinda ya kira 'yan ta'adda daga kasar
Shugaba Bashar al-Assad na kasar Sham, wanda ya lashi takobin kawar da abinda ya kira 'yan ta'adda daga kasar
Shugaba Bashar al-Assad na kasar Sham ya lashi takobin raba kasar da abinda ya kira "'yan ta'adda" a yayin da dakarun tsaro suke ci gaba da gwabzawa da 'yan tawaye wadanda suka yi kokarin kwace wasu sassan biranen Aleppo da Damascus.

Kafofin yada labarai na gwamnatin Sham sun ambaci shugaba Assad yana fadi jiya talata cewa ba zai nuna sassauci ga 'yan ta'adda ba. Ya gana da sakataren Majalisar Tsaron kasa ta Iran, Saeed Jalili, wanda ya kai ziyara kasar ta Sham.

Gidan telebijin na kasar Sham ya nuna ganawar tasu, wanda kuma shi ne karon farko da aka ga shugaba Assad a telebijin cikin makonni biyu.

Jalili yayi alkawarin cewa Iran zata ci gaba da goyon bayan kasar Sham, wanda yace tana daya daga cikin ginshikan yin adawa da abokan gaba na kasashen waje.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: habeeb dalha Daga: dawakin kudu kano
15.08.2012 17:41
Ina ganin yakin siriya zai jawo yak yake a kasashen gabas ta tsakiya chiki har da kaiwa israila hari.


by: Mohammed rahman Daga: Jalingo taraba state
08.08.2012 07:58
Haba shugaba assad kamata yay kasauka tunda bagadobane koda a samu zamanlafiya da kwanchiyar hankali akasarka bawaiza a tsaya anakashe rayukan bayin Allah ba

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti