Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama Ya Kammala Hada Hancin Majalisar Tsaro


Shugaban Amurka Barack Obama da wadanda ya zaba su rike manyan mukaman tsaron kasa
Shugaban Amurka Barack Obama da wadanda ya zaba su rike manyan mukaman tsaron kasa
Shugaban Amurka Barack Obama yana kammala hada hancin majalisar da zata kula da harkokin tsaro na kasa a wa’adin mulkinsa na biyu, tare da yin kira ga majalisar dattijai ta gaggauta amincewa da wadanda ya zaba su shugabanci ma’aikatar tsaro da kuma hukumar leken asirin Amurka.

Jiya Litinin Mr. Obama ya zabi tsohon dan majalisar dattijai dan jam’iyar Republican, Chuck Hagel a matsayin sakataren tsaro da mai ba shi shawarwari kan yaki da ayyukan ta’addanci John Brennan a matsayin shugaban hukumar leken asirin Amurka –CIA.

Shugaba Obama ya bayyana Hagel a matsayin “shugaban da ya cancanta dakarunmu su samu.” Ya kuma ce tsohon dan majalisar mai wakiltar jihar Nebraska ya nuna irin al’adar yin aiki ba tare da kula da banbancin jam’iya ba da ake bukata matuka a Washington.

Mr. Obama ya kuma yabawa Brennan sabili da jagorantar yunkurin murkushe kungiyar al-Qaida yayinda yaci gaba da kare akidojin da suka shata alkiblar Amurkawa.

Hagel da Brennan duka suna bukatar amincewar majalisar dattijai inda tuni wadansu suka fara bayyana rashin amincewarsu da gabatar da sunayensu.
XS
SM
MD
LG