Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Haiti Ya Sauka Daga Mulki Domin Bin Dokar Kasa


Haiti's outgoing President Michel Martelly delivers a goodbye salute to supporters before tucking into his vehicle outside the parliament building in Port-au-Prince, Haiti, Sunday, Feb. 7, 2016.
Haiti's outgoing President Michel Martelly delivers a goodbye salute to supporters before tucking into his vehicle outside the parliament building in Port-au-Prince, Haiti, Sunday, Feb. 7, 2016.

Shugaban kasar Haiti Michel Martelly da ya sauka daga mulkin a jiya Lahadi kamar yadda kundin tsarin mulki ya bukace shi da yi, bayan mulkinsa na shekaru 5 ba tare da an zabi wanda zai maye gurbinsa ba.

Gabanin saukar shugaban, wanda tsohon mawakin kade-kaden Turawa ne, ya fadawa ‘yan Majalisar Haiti a birnin Port-Au-Prince cewa, zai sauka daga mulkin ne don ya bada tasa gudunmawar ga daidaiton kundin tsarin mulkkin kasarsu.

Inda ya mika ragamar mulkin kasar ga ita Majalisar da ke da tsananin tsaro, inda kuma ake jiran jin wanda ‘yan Majalisar za su zaba don ba shi rikon kwaryar mulki kafin lokacin da ya kamata a yi zaben shugaba na saosai.

Har ya zuwa yammacin Lahadin jiya din dai, ba wani kwakkwaran bayanin wanda zai gaji mulkin kasar mai fama da talauci don jan ragamarta na ‘yan wasu watanni zuwa lokacin zabe a kasar.

XS
SM
MD
LG