Zakarun kwallon kafa na nahiyar Turai, Spain, ta sha kashi da ci daya mai ban haushi a hannun 'yan wasan kasar Switzerland a gasar cin kofin duniya a Afirka ta Kudu.
Wannan nasarar farko da kasar Switzerland ta taba samu a gasar cin kofin duniya, kuma a kan kasar Spain, ita ce abar ba-zata mafi girma da aka gani zuwa yanzu a gasar cin kofin kwallon kafar duniya da ake yi a Afirka ta Kudu. Spain ta kanainaye wasan, amma kuma 'yan tsaron baya na Switzerland sun hana su ketawa.
A bayan da Eren Derdiyok na Switzerland ya koro kwallo, sai Gelson Fernandes ya jefa ta cikin raga a minti na 52 da fara wasa.
Haka aka tashi daga wannan wasa da ci daya da babu.
Zuwa uimawa, mai masaukin baki Afirka ta Kudu zata kara da Uruguay a wasanta na biyu a rukunin farko. Dukkan kasashen dake wannan rukuni su na da maki dai-daya.