Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TEKUN LIBYA: Jirgin Ruwa Dauke da Bakin Haure 700 Ya Kife


Wasu bakin haure da aka ceto jiya Lahadi
Wasu bakin haure da aka ceto jiya Lahadi

Kasar Italiya tana kaddamar da aikin ceto wadanda suke cikin jirgin da ya kife a gabar tekun kasar Libya

Kasar Italiya ta kaddamar da gagarumin aikin nema da ceton rayuka a kogin Baharum bayan da jirgin ruwa ‘dauke da ‘darurruwan bakin haure ya kife cikin dare a gabar tekun Libya. Ana kyautata zaton mutane kusan 700 ne suka mutu.

Kafin faduwar rana jiya Lahadi, jami’ai sun ce an sami ceton mutane 28 amma ana kyautata zaton daruruwa sun mutu a ruwa dake tazarar kilomita 200 daga kudu da kudancin tsibirin Lampedusa na kasar Italiya. Ma’aikatan ceton rayukan sunce yawancin mutanen da suka ‘bace sun makale ne a cikin jirgin mai tsawon mita 20karkashin teku.

Idan har haka ta tabbata, adadin mutanen da suka mutu cikin kogin Baharum a wannan shekara ta 2015, ya haura 1,500.

Manazarta sunce suna tsammanin fataucin mutane ta kogin Baharrum, zai kara muni a watanni masu zuwa, yayinda yanayin rashin matsanancin sanyi, da hangen zaman lafiya da wadata na turai, ke janyo hankulan bakin haure daga Afirka dama sauran kasashe.

XS
SM
MD
LG