Juma'a, Mayu 29, 2015 Karfe 01:00

Afirka

Za a Ci Gaba Da Zabe A Wadansu Mazabu Yau A Ghana

Wani yana wucewa kusa da hotunan 'yan takara a GhanaWani yana wucewa kusa da hotunan 'yan takara a Ghana
x
Wani yana wucewa kusa da hotunan 'yan takara a Ghana
Wani yana wucewa kusa da hotunan 'yan takara a Ghana
Hukumar zabe ta kasar Ghana ta kara lokacin kada kuri’a a babban  zabe na kasa da aka gudanar jiya inda wadanda basu iya kada kuri’a ba, sakamakon wadansu muhimman dalilai zasu je su jefa kuri’unsu.

Kwamishinan zabe na kasar Ghana ya bayyana cewa, za a ci gaba da gudanar da zabe yau asabar a wadansu runfuna sakamakon tangarda da aka samu da wadansu na’urorin da suka hana masu kada kuria da dama yin zabe.

Wannan ne karon farko da hukumar zaben kasar Ghana take amfani da wani sabon salo inda injuna suke tantance masu rajista ta wajen gwada yatsunsu.
An ci gaba da kirga kuri’u a mazabun da ba a sami tangarda ba.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti