Jumma’a, Mayu 06, 2016 Karfe 08:17

  Labarai / Sauran Duniya

  Zanga-Zanga Tana Bazuwa A Kasashen Musulmi

  A yayin da ake kara nuna fusata kan wani faifan bidiyo na nuna kin jinin addinin Islama da yin batunci ga Annabi Muhammad (saw)

  'Yan zanga-zanga su na kaucewa daga barkonon tsohuwar da 'yan sanda suka jefa musu a al-Qahira ta Misra.'Yan zanga-zanga su na kaucewa daga barkonon tsohuwar da 'yan sanda suka jefa musu a al-Qahira ta Misra.
  x
  'Yan zanga-zanga su na kaucewa daga barkonon tsohuwar da 'yan sanda suka jefa musu a al-Qahira ta Misra.
  'Yan zanga-zanga su na kaucewa daga barkonon tsohuwar da 'yan sanda suka jefa musu a al-Qahira ta Misra.
  An barke da sabbin zanga-zanga yau jumma'a a fadin kasashen Musulmi, inda ake kara nuna fusata kan wani faifan bidiyo na nuna kin jinin addinin Musulunci wanda aka sanya a Intanet.

  Zanga-zanga ta baya-bayan nan ta barke a Tunis, babban birnin kasar Tunisiya, inda 'yan sanda suka harba barkonon tsohuwa kan 'yan zanga-zanga dake jifa da duwatsu. Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun samu nasarar tsallaka katangar da ta kewaye ofishin jakadancin.

  Har ila yau, wannan fitina ta yadu zuwa kasar Sudan, inda shaidu suka ce 'yan sanda sun yi arangama da  dubban 'yan zanga-zanga da suka doshi ofishin jakadancin Amurka a Khartoum. An bayar da rahoton cewa 'yan zanga-zanga sun samu sukunin shiga cikin harabar ofishin jakadancin kasar Jamus.

  Jumma'a ce rana ta hudu da fara yin zanga-zanga a kan wannan fim, wanda ya zamo batun da aka yi ta magana a kai a lokacin sallar Jumma'a a fadin Gabas ta Tsakiya, da yankunan kudanci da gabashin Asiya da kuma nahiyar Afirka. Da yawa daga cikin 'yan zanga-zangar su na kai farmaki ne a kan kasashen da suke gani ba su dauki kwararan matakan hana yin wannan fauifan bidiyo ba.

  Ofisoshin jakadancin Amurka da na kasashen ketare sun kara irin matakan tsaron da suke dauka a bayan da aka fara yin wannan zanga-zanga ranar talata.

  Wuraren da aka gudanar da zanga-zanga mafiya girma sun hada da birnin al-Qahira a Masar, inda a yau jumma'a 'yan zanga-zanga suka yi arangama da 'yan sanda dake harba barkonon tsohuwa.

  Watakila Za A So…

  Harin Syria kan sansanin yan gudun hijira ya kashe mutane 30

  Sa'o'i kadan bayan jami'an Rasha da Syria sun tabbatar da tsagaita wuta a birnin Aleppo sai jiragen yaki na Syria ko Rasha suka soma ruwan bamabamai kimanin kilimita 30 daga birnin lamarin da ya kaiga hasarar rayuka 30 Karin Bayani

  Sauti Shugaba Umaru Musa Yar'adua ya jagoranci Najeriya bilhaki da gaskiya - Jonathan

  Shekaru shida ke nan da Allah ya yiwa tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa Yar'adua rasuwa, rasuwar da ta kaiga mataimakinsa Goodluck Jonathan daga yankin Niger Delta ya dare kan mulki Karin Bayani

  Wasu mayakan sa kai sun farma kamfanin hakan man fetur na Chevron a Niger Delta

  Rundunar sojojin ruwan Najeriya ko Navy ta sanar jiyar Alhamis cewa wasu mayakan sa kai sun farma kamfanin hakan man fetur na Chevron a matsayin wani hari na baya bayan nan da suka aiwatar a yankin Niger Delta Karin Bayani

  Kakakin Majalisar Wakilan Amurka yace ba zai iya goyon bayan Trump ba

  Kodayake hamshakin attajirin nan Donald Trump shi kadai ne dan takarar shugabancin Amurka daga jam'iyyar Republican ya rage, kakakin majalisar wakilan Amurka shi ma dan jam'iyyar Republican yace ba zai iya goyon bayan attajirin ba. Karin Bayani

  Sauti Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar kubuto wasu mutane a dajin Sambisa

  A cigaba da yakin da sojojin Najeriya keyi da 'yan ta'adan Boko Haram, rundunar soji ta bakawai dake Maiduguri ta samu nasarar kubuto wasu mutane da dama daga dajin Sambisa Karin Bayani

  Sauti Majalisar dokokin Nijar ta amince a ciwo bashi domin inganta wutar lantarki a karkara

  A karkashin dokokin da majalisar ta amince dasu kimanin biliyan goma sha shida na kudaden sefa ne gwamnatin ta Nijar zata ranto daga bankin cigaban Afirka ta yamma domin inganta wutar lantarki a yankunan karkarar kasar Karin Bayani

  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye