Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Karrama Zaratan Dakarun Rundunar Sojojin Najeriya Da Aka Kashe A Delta Da Lambar Girmamawa Ta Kasa


Zaratan Dakarun Rundunar Sojojin Najeriya
Zaratan Dakarun Rundunar Sojojin Najeriya

Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karama zaratan dakarun Rundunar Sojojin Najeriya da wadansu batagari dake kauyen bakin teku suka yiwa kisan gilla da lambar girmamawa na kasa.

WASHINGTON DC - Shugaba Tinubu ya kuma ba da umarni a biya iyalansu duk kudadensu cikin tsawon kwanaki 90 da yin tayin daukar nauyin karatun 'ya'ya da kuma bada gidaje ga iyalan sojojin da aka hallaka.

Hakan ya faru ne yayin da ake birne gawawwakin Kwamandan Bataliyar Sojin Najeriya ta 181 da wasu Manjo-Manjo 2 da kyaftin guda da kananan sojoji 12 a makabartar sojoji.

A yau Laraba 27 ga watan Maris din da muke ciki aka kawo gawawwakin sojojin da aka yiwa kisan gilla zuwa Makabartar Sojin Najeriya dake Abuja domin birnewa.

An yi jana'izar sojojin da wadansu batagari dake kauyen bakin teku suka yiwa kisan gilla yayin da suke gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya tsakanin al'umomin Ukuoma dana Okuloba dake yankin a bisa girmamawar aikin soja mafi girma.

Cikin mahalarta bikin jana'izar harda, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa da takwarorinsa na Sojin Kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja dana Sojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar dana Sojin Ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da kuma Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas.

Suma gwamnonin jihohin Delta, Sheriff Oborevwori dana Bayelsa, Duoye Diri dana Kogi, Usman Ododo dana Kaduna, Uba Sani dana Imo, Hope Uzodinma dana takwararsu na Kano, Abba Kabir Yusuf sun halarci jana'izar.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya isa taron jana'izar da misalin karfe 4 da mintuna 10 na yammacin yau.

An yi wa sojojin 17 da kisan gilla a ranar 14 ga watan Fabrairun daya gabata a kauyen Okuama dake karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG