Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kogi Tace Tana Kokarin Kubutar Da Daliban Jami’ar Jihar Da ‘Yan Bindiga Suka Sace


'Yan bindiga
'Yan bindiga

‘Yan bindigar dai sun afkawa jami’ar kimiyya da fasaha ne dake garin Osara a karamar Hukumar Adabi a jihar Kogi inda bayan jikkata wasu daliban, sannan sukayi garkuwa da wasu kimanin 57.

Malam Dan Asabe wani mazaunin jihar Kogi yace ‘yan bindigar sun haura cikin jami’ar ne ta baya suka dinga harbin kan mai uwa da wabi kamar yadda ya yiwa wakilin Muryar Amurka bayani ta wayar salula.

Tuni dai Gwamnatin jihar Kogin tayi Allah wadai da wannan hari tare da nuna takaicinta akan lamarin.

Kwamishinan Labarai na jihar Kogin, Kensly Fanwo, yace, kawo yanzu basu tantance adadin daliban da ‘yan bindigar suka sace ba, amma sun hada hannu da jami’an tsaro domin ganin an kubutar da daliban cikin koshin lafiya.

Ya kara da cewa, a lokacin da gwamnatin jihar ta samu labarin tayi kokarin jibga jami’an tsaro a wannan yanki domin samun nasarar kubutar da daliban da aka sace.

A wata sanarwa daga kakakin ‘yan sandan jihar Kogin, Wilyans Aya, ya ce kwamishinan ‘yan sandan ya kara tura jami’an tsaro na musamman domin samun nasarar kubutar da daliban.

Garkuwa da daliban makaranta dai na ci gaba da daukar hankali a Nijeriya, al’amarin da masana suka ce babbar barazana ce a bangaren Ilimi a kasar.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

Gwamnatin Jihar Kogi Tace Tana Kokarin Kubutar Da Daliban Jami’ar Jihar Da ‘Yan Bindiga Suka Sace
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG