Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taimaka wa Yara na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Rotary .


Taimaka wa Yara na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Rotary .
Taimaka wa Yara na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Rotary .

<!-- IMAGE -->

A cewar jami'an WHO na hadin gwiwar kasashe alamar yin nasara a yaki da cutar polio ta ta'allaka ne kan irin dinbin nasarar da a ka yi a Nijeriya inda al'amura suka dan ingantu game ta yawan yaran da ake nasarar yi masu riga kafin polio, da kuma yadda matsalar da ake samu saboda al'ada ta ragu saboda taimakawa da shuwagabannin addini da na al'umma su ke yi.

Har yanzu Nijeriya na daya daga cikin kasashen da polio ta fi addaba a duniya wacce don haka ta zama daya daga cikin kasashen da aka fi mai da hankali a kansu ganin irin yadda ta ke da masu dauke da cutarwajen 450 wanda kenufin kashi 75cikin dari na yawan cutar ta polio a sashen na Afirka.

Cikin kimanin yara 400 da sukan kamu da polio akan sami akalla guda da kan sami nakasa. Kuma daga cikin yara masu nakasar, guda 10 zuwa 15 kan mutu saboda matsalar nakasar jijiyoyin numfashi, a fadin WHO.Duk da haka dai a iya cewa ya zuwa yanzu cutar polio ta ragu da kashi 99 cikin dari tsakanin 2001 da 2009.

XS
SM
MD
LG