Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Aikin Yin Allurar Riga-kafin Coronavirus A Nijar


Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun kaddamar da kamfen din allurar riga-kafin cutar coronavirus domin shiga sahun kasashen da suka yi na’am da allurar riga kafi a matsayin hanya mafi inganci wajen yaki da wannan cuta da ta addabi duniya.

Firai minista Brigi Rafini ne ya fara karbar allurar a wannan kamfe yayin wani bikin da ya gudana a asibitin kwararru na Hospital General de Reference a birnin Yamai.

Allurar riga kafi
Allurar riga kafi

A cewarsa, allurar ita ce hanya mafi a’ala wajen kare kai daga kamuwa da wannan masifa.

Tuni aka ware wasu cibiyoyin na musamman a manyan biranen wannan kasa domin gudanar da ayyukan wannan kamfe wanda zai shafi wani rukuni na al’uma a zagayen farko kafin nan da mako 4 a sake yi masu wata allurar a zagaye na 2 in ji ministan kiwon lafiya Ahmed Boto.

Likitoci sun kara nanata gamsuwa da nau’in wannan allura da ta fito daga kasar China saboda a cewarsu ba wata tantama a game da kwarewar wadanda suka yi wannan aiki.

Wani jami’i a ma’aikatar lafiya ta kasa Zabeirou Souley ya karbi tasa allurar a wunin farko na wannan kamfe ya kuma bayyana mana dalilansa na shiga sahu.

A ranar Lahadin 21 ga watan Maris ne shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou mai shirin barin gado ya karbi rukunin farko na tallafin allurar riga- kafin cutar corona daga hannun jakadan kasar China wadanda aka kIyasta cewa ya kimanin 40,0000 ne da za a yi wa mutun 20,0000 kafin a nan gaba a samar da kari daga abokan hulda na waje.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

XS
SM
MD
LG