Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Daukar Matakan Tsaro a Birtaniya


Birtaniya ta kure mizanin barazanar kai mata harin ta’addanci, inda ta tura dakarun soja domin su taimakawa ‘yan sanda, a cewar Fara Minista Theresa May jiya Talata.

May ta yiwa ‘kasar jawabi, kwana guda bayan da ‘dan kunar bakin wake ya tada nakiyar jikinsa a wajen da mawakiya Ariana Grande ta yi wasa a Manchester, ya kashe mutane 22 da kuma raunata wasu sama da 60. Ta ce daga yanzu za a rika tura dakarun soja domin su taimakawa ‘yan sanda a wasu muhimman hidimomi ciki har da guraren wasannin kwallon ‘kafa da guraren wake-wake.

Fara Ministar ta ce ‘kasar ta ‘kure mizanin barazanar kai mata hare-haren ta’addanci, wanda hakan ke nufin tana iya fuskantar ‘karin samun hare-hare.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG