Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Mutum 30 Daga Cikin Daliban Yawuri Da Aka Sace A Kebbi


Gwamna Bagudu (Twitter/Bagudu)
Gwamna Bagudu (Twitter/Bagudu)

A ranar 17 ga watan Yuni ne 'yan bindigar suka kai farmaki a makarantar da ke garin na Yawuri, mai tazara kilomita kusan 200 da babban birnin jihar ta Kebbi, inda suka yi awon gaba da dalibai kusan 63.

Gwamnatin Jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar sako dalibai 30 daga cikin daliban da 'yan bindiga suka sace a kwalejin gwamnatin tarayya ta Birnin Yawuri.

A ranar 17 ga watan Yuni ne 'yan bindigar suka kai farmaki a makarantar da ke garin na Yawuri, mai tazara kilomita kusan 200 da babban birnin jihar ta Kebbi, inda suka yi awon gaba da dalibai kusan 63.

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya ce za a duba duba lafiyar daliban kafin a mika su ga iyayensu yayin da ake kokarin a ga cewa an kubutar da sauran da suka rage.

Hukumomin jihar sun ce dalibai 27 da malamai biyu da wani jami’in gudanarwa na makarantar ta FGC Yawuri aka sako.

Sanata Adamu Aliero (Twitter/Gwamnatin Ogun)
Sanata Adamu Aliero (Twitter/Gwamnatin Ogun)

Gabanin sanarwar da gwamnati ta yi, dan majalisar dattawa daga jihar ta Kebbi, kuma tsohon gwamna Adamu Aliero ya tabbatar da sakin daliban, a zantawar da ya yi da Muryar Amurka.

“An sako mana mutum 30, har yanzu akwai guda 33 wadanda ba a sako sub a.” In ji Aliero.

Tun a baya dai maharan dasuka sace daliban sun ce ba kudin fansa suke bukata ba a cewar Aliero.

“Abin da suke so shi ne ya za a yi a zauna da su a samu zaman lafiya, ba a yankin jihar Kebbi kadai ba har ma Zamfara, Sokoto, Katsina, Kaduna da Neja.”

Saboda haka, a cewar Aliero ba a biya ko kwabo ba wajen karbo wadannan dalibai.

Sanatan ya ce za a ci gaba da tattaunawa da su har sai an kai ga sako sauran daliban da ke hannun ‘yan bindigar.

XS
SM
MD
LG