Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ayyukan 'Yan Bindiga: Gwamnatin Zamfara Ta Sanya Dokar Hana Zirga-Zirga Akan Iyakokin Sokoto Da Katsina


Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Radda
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Radda

Gwamnatin Zamfara ta bada umarnin gaggauta takaita zirga-zirga akan iyakar jihar da jihohin Sokoto da Katsina tun daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safiya saboda karuwar hare-haren 'yan bindiga akan matafiya.

WASHINGTON DC - Gwamnatin Zamfara ta bada umarnin gaggauta takaita zirga-zirga akan iyakar jihar da jihohin Sokoto da Katsina tun daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safiya saboda karuwar hare-haren 'yan bindiga akan matafiya.

Kwamishinan Yada Labarai da Al'adu na jihar Zamfara, Munnir Haidara ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda yace takaita zirga-zirgar na daga cikin shawarwarin da aka cimma yayin taron majalisar tsaron jihar.

Ya kara da cewar, daga yau, gwamnatin jihar nan ta bada umarnin takaita zirga-zirga akan iyakar 'yan kara inda Zamfara tayi iyaka da jihar Katsina da kuma iyakar Bimasa inda muka iyaka da jihar Sokoto tun daga karfe 7 na yammaci zuwa 6 na safe.

Kwamishinan yace, an yi hakan ne da nufin dakile yawan satar matafiya akan babbar hanyar data tashi daga Sokoto ta wuce ta gusau zuwa Funtua.

A cewarsa, ana umartar dukkanin masu ababen hawa da matafiya su kiyaye wannan doka, kasancewar an umarci hukumomin tsaro su sa idanu akan iyakokin 2 domin tabbatar da aiwatar da ita.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG