Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bai Kamata A Sha Giya A Bugu Ko A Tada Hankali Ba A Lokacin Bikin Kirsimeti – Ravaran Ogah


Reverend Abraham Ogah
Reverend Abraham Ogah

Lokacin sha, ya kamata a sha lemu ba giya ba. Ba lokaci ba ne da za’a sha a bugu ba, kuma ba lokaci ba ne da za a tada hankalin mutane.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Kirisotci a Jihar Borno, Ravaran Abraham Ogah ya yi kira ga mabiya addinin Kirista da su yi bukukkuwan Kirsimeti cikin godiya da addu’a domin yin murnar zagayowar ranar haihuwar Isa Almasihu.

Ravaran Ogah ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da Muryar Amurka a birnin Maiduguri da ke jihar Barno, inda ya ce bai kamata asha giya a bugu ko a tada hankali ba a lokacin bikin Kirsimeti.

Ya ce ‘‘lokacin biki, ya kamata a yi biki. Lokacin cin abinci, ya kamata a ci abinci. Lokacin sha, ya kamata a sha lemu ba giya ba. Ba lokaci ba ne da za’a sha a bugu ba, kuma ba lokaci ba ne da za a tada hankalin mutane.

‘’Wannan lokaci ne da Yesu Kiristi y ace mu kaunaci juna kuma ya kamata mu taimakawa wayanda bas u da karfi mu kai musu ziyara da abinci. In da kudi mu taimaka musu. Idan akwai kudi, ya kamata mu shiga asibiti mu gaida marasa lafiya mu taimake su da abun sha da abinci. Haka ma ya kamata mu yi wa wadanda ke kurkuku’’, a cewarsa.

Mabiya addinin Kirista a fadin duniya na bikin Kirsimeti da aka saba gudanarnwa a rana ta 25 ga watan Disamba.

Latsa wannan bidiyo don jin cikakkiyar hirarsa da Sahen Hausa na Muryar Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG