Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barazanar Yaki Tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu na Karuwa


Sojojin Koriya ta Kudu na Atisaye
Sojojin Koriya ta Kudu na Atisaye

Koriya ta Arewa da ta Kudu sun kara zafafa cacar bakin da su ke yi da juna, a daidai lokacin da Koriya ta Kudu ta kara gudanar atisayen sojoji.

Koriya ta Arewa da ta Kudu sun kara zafafa cacar bakin da su ke yi da juna, a daidai lokacin da Koriya ta Kudu ta kara gudanar atisayen sojoji.

Koriya ta Arewa ta fadi jiya Alhamis cewa a shirye ta ke fa ta yi amfani da makaman nukiliyarta a abin da ta kira, “Yakin day a wajaba” muddun aka cakune ta. Ministan Sojojin Kasar Kim Yong Chun ya ce Koriya ta Kudu na kokarin tsokano yaki ne da gangan.

Shugaban Koriya ta Kudu Lee Myung-bak ya ziyarci wani sansanin sojin da ke kusa da kan iyaka jiya Alhamis, inda ya ce Koriya ta Kudu za ta maida martani kan duk wani harin Koriya ta Arewa da matukar karfi. Mr. Lee ya ce rashin sani ne ya sa abaya ya yi tsammanin cewa hakuri ka iya kawo kwanciyar hankalin a yankin ruwayen na Koriya.

Sojojin Koriya ta Kudu na sama da na kasa sun gudanar da atisayensu na baya-bayan nan jiya Alhamis, inda su ka yi ta luguden wuta kan wani kwari mai cike da dusar kankara mai nisan kilomita 30 kawai daga kan iya ta amfani da bama-bamai da albarusan da tankoki su ka yi ta harbawa da bindigogin atilare da rokoki da kuma jaragen yaki samfurin F-15.

Tsohon jami’in diflomasiyyar Amurka Bill Richardson wanda kwanan nan ya dawo daga Koriya ta Arewa ya gaya wa VOA jiya Alhamis cewa al’amarin fa ya yi tsauri sosai ta yadda da bukatar a kara shigar da harkar diflomasiyya ciki. Ya ce ya na marmarin ganmin maido da tattaunawa ta masu ruwa da tsaki shida da ta hada da Koriya ta Arewa da sauran manyan kasashen yanki-yanki. Richardson ya bayyana al’amarin na mashigar ruwan Koriyar da cewa tamkar tokar bindiga ce don haka ya ce abinda ke da muhimmanci a yanzu shi ne sake tattaunawa.

Fadar White House ta fadi a farkon wannan satin cewa babu ko alamar cewa Koriya ta Arewa na shirin shiga sabuwar tattaunawar ta masu ruwa da tsaki shida din.

XS
SM
MD
LG