Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CBN Ya Umarci Bankuna Su Caji Kashi 0.5 Cikin 100 A Matsayin Harajin Tsaron Intanet


Babban bankin Najeriya CBN
Babban bankin Najeriya CBN

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da CBN din ya fitar wacce aka rabawa ilahirin bankunan kasuwanci dana bunkasa cinikayya da marasa ta’ammali da kudin ruwa dana biyan kudin ayyuka dana tafi da gidanka.

Babban Bankin Najeriya (CBN)ya umarci bankunan kasar su fara cazar kashi 0.5 cikin 100 a matsayin harajin tsaron kafar sadarwar intanet akan duk hada-hadar da suka yi.

A cewar babban bankin za’a fara cirar harajin ne makonni 2 bayan fitar da sanarwar.

Rukunin hada-hadar da aka tsame daga wannan harajin sun hada dana bayarwa ko biyan bashi da biyan albashi da aikewa da kudi tsakanin mabambantan asusun ajiya a cikin banki daya da kuma tsakanin mabambantan bankuna amma akan abokin hulda daya da kuma aikewa da kudi tsakanin mabambantan abokan hulda amma a banki daya.

Sauran wadanda aka tsame daga harajin sun hada da aikewa da kudi tsakanin rassan banki guda da biya da sasanta biyan kudi ta hanyar chaki da sauran takardun biyan kudi ta banki dana hada-hadar data shafi karfafa jarin banki wacce zata shafi matsar da makudan kudade daga inda za’a karbo su dana tsimi da tanadi da zasu kunshi ajiya mai dogon wa’adi da makamantansu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG