Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar shan inna ta sake bulla a jihar Kaduna


Mutanen jihar Kaduna inda aka sami bullar cutar shan inna
Mutanen jihar Kaduna inda aka sami bullar cutar shan inna

Binciken ma’aikatan lafiya na nuni da cewa, an sami bullar cutar a garin Maiyashi cikin karamar hukumaar Birnin Gwari

Murnar gwamantin jihar Kaduna ta shawo kan cutar shan inna ta koma ciki ba da dadewa ba bayanda wargidan gwamnan jihar Mrs Amina Ibirahim Yakowa ta jagoranci bukin cika shekara hudu ba tare da samun billar cutar shaninna a fadin jihar ba.

Binciken ma’aikatan lafiya ya gani cewa, an sami bullar cutar a garin Maiyashi cikin karamar hukumaar Birnin Gwari.

Bisa ga rohotanni Fulani makiyaya da suka fito daga jihar Zanfara ne suka zo da dansu dauke da cutar suka yada zango a kyauyen na Maiyashi dake karamar hukumar Birnin Gwari.

Ita dai jihar Kaduna ta shafe tsawon shekara hudu ba tare da samun ko yaro daya dauke da cutar shan inna ba.

Jami'in kiwon lafiya na karamar hukumar ta Birnin Gwari, Abdulrahman Yahaya wanda ya tabbatar da bullar cutar, ya jadada cewa, makiyayan da suka fito ne daga jihar Zanfara suka shigo da cutar.

A nashi bayanin, shugaban karamar hukumar Birnin Gwari Dahiru Adamu, ya nuna rashin jin dadin shi game da samun bullar cutar a garin na Maiyashi. Ya kuma tabbatar da cewar za suyi dukan abinda ya dace domin ganin sun shawo kan sake shigo da cutar daga makwabta.

Tuni tawagar jami'an majalisar dinkin duniya suka isa kyauyen domin tantancewa, da kuma fadakar da jama'a game da mahimmancin yin rigakafin cututtukan da ke kama kananan yara.

Hukumomin Nageriya sun bada tabbacin cewar za'a kawas da yaduwar cutar shan inna kafin karshen shekara ta 2013.

XS
SM
MD
LG