Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Lafiya ta duniya tace an sami raguwar masu rasuwa da cutar Malariya


Sauro mai haddasa zazzabin malariya
Sauro mai haddasa zazzabin malariya

Rahoton hukumar lafiya ta duniya na nuni da cewa, an sami raguwar mutuwa da zazzabin cizon sauro a shekara ta dubu biyu da goma.

Rahoton shekara-shekara da hukumar lafiya ta duniya ta fitar na shekara ta dubu biyu da goma na nuni da cewa, an sami raguwar mace mace ta dalilin kamuwa da zazzabin cizon sauro. Bisa ga rahoton an sami raguwar mace macen da kashi 25% a duk fadin duniya tun cikin shekara ta dubu biyu, yayinda aka sami raguwar mace macen zazzabin cizon sauro a yankin Afrika da kashi 33%.

Hukumar lafiya ta duniya ta yi kiyasin cewa, mutane dubu shida da dari biyar suka mutu sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro kashi tamanin da shida na adadin kuma kananan yara ne da shekarunsu suka gaza biyar. Kashi 60% na masu mutuwar da zazzabin cizon sauron kuma daga kasashen Najeriya da Damokaradiyar jamhuriyar Kwango da Burkina Faso da Mozambique da Cote d’Ivoire da kuma Mali suke.

Dr Margaret Chan babbar darektar Hukumar lafiya ta duniya tace, “Muna samun ci gaba ainun a yaki da cutar da ta zama da kalubalar gaske a harkokin lafiya. Mun sake samun ci gaba a yaki da cutar zazzabin cizon sauro a cikin shekara ta dubu biyu da goma da ya taimaka wajen rage mace mace ta dalilin kamuwa da zazzabin cizon sauro, sai dai akwai alamun dake nuni da cewa, yana yiwuwa a sami koma bayan wannan ci gaba”

Hukumar lafiya ta duniya ta bada tabbacin cewa, kasashe hudu sun shawo kan matsalar zazzabin cizon sauro tun daga shekara ta dubu biyu da bakwai, yayinda Amermenia ta shiga sahun kasashen a watan Oktoba bara. Dr. Chan ta bayyana cewa, akwai hanyoyin yaki da zazzabin cizon sauro masu arha da suke da inganci.

Sai dai tace babbar kalubalar da suke fuskanta ita ce, ci gaba da samun tallafin kudin aikin, tace suna bukatar tallafin kudi a asusun na duniya da sababbin masu tallafi da kuma ganin kasashen da cutar ta zama annoba sun dauki matakan takalar kalubalar dake gabansu. Bisa ga cewar darektar hukumar lafiya ta duniya, za a bukaci sake miliyoyin gidajen sauro a cikin shekaru masu zuwa yayinda ake bukatar na’urorin gwaji da kuma hanyoyin jinya masu inganci.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG