Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Cire Babban Sufeton 'Yan Sanda Mohammed Adamu


Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu.
Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana dalilin cire Babban Sufeto Janar na ‘Yan sanda Mohammed Abubakar Adamu, tare da maye gurbinsa tun kafin karewar wa’adin wata 3 da shugaba Buhari ya kara masa.

Sanarwar nadin sabon mukaddashin sufeto-janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ta zo wa ‘yan kasar a ba zata, musamman saboda karin wa’adin watanni 3 da shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa shugaban ‘yan sanda mai barin gado Mohammed Adamu, bayan karewar wa’adin mulkinsa.

An nada Adamu a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya ne a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 2019, a yayin da wa’adin mulkinsa ya kai karshe a ranar 1 ga watan Fabrairun wannan shekara ta 2021.

Sabon Sufeton 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu Abubakar
Sabon Sufeton 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu Abubakar

To sai dai kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya kara tsawaita masa lokaci da karin watanni 3, bisa tanadin sashe na 15(A) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, sabon wa’adin da zai kai karshe a ranar 1 ga watan Mayu mai zuwa.

Karin bayani akan: Mohammed Adamu Abubakar, Usman Alkali Baba, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Matakin na shugaban kasa na tsawaita wa’adin babban sufeto Adamu ya janyo cece-kuce, inda ‘yan Najeriya da dama suka nuna rashin gamsuwa da matakin, musamman a wancan lokacin da ake ta kiraye-kiraye ga shugaban kasa da ya sauya manyan hafsoshin tsaron kasar, da kuma babban sufeton ‘yan sandan, sakamakon kara tabarbarewar lamurran tsaro a yankunan kasar daban-daban.

To sai dai kwatsam a ba zata, aka ji sanarwar nadin sabon Babban Sufeton da zai maye gurbin Adamu, wanda wasu rahotannin suka bayyana cewa yana kan ziyarar aiki a jihar Imo a lokacin da aka ba da sanarwar.

DIG Usman Alkali Baba
DIG Usman Alkali Baba

Da yake karba tambayoyin ‘yan jarida jim kadan bayan ya ba da sanarwar sabon babban sufeton na ‘yan sanda a fadar shugaban kasa, Ministan lamurran ‘yan sanda Muhammadu Maigari Dingyadi, ya ce sabon nadin ya biyo ne "bayan kammala kwakkwaran Nazari da bincike akan wanda ya cancanta ya dare kan mukamin."

Dingyadi ya ce “akwai jerin sunayen zarata kuma hazikan jami’an ‘yan sanda masu mukamin AIG da DIG da aka gabatar domin zaben sabon shugaba a cikinsu, daidai da tanadin sashe na 7, karamin sashe na 2 na dokar ‘yan sandan Najeriya ta shekara ta 2020.”

Ministan Lamurran 'yan Sanda Muhammadu Maigari Dingyadi
Ministan Lamurran 'yan Sanda Muhammadu Maigari Dingyadi

Wannan, a cewar Ministan, shi ne dalilin da ya sa aka sami jinkiri bayan karewar wa’adin mulkin Adamu, domin yin Nazari akan wanda ya fi dacewa ya gaje shi.

“Bayan la’akari da wanda yafi gogewa da sanin makamar aiki, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Usman Alkali Babaa a matsayin sabon mukaddashin babban sufeton ‘yan sanda, wanda zai soma aiki nan take,” in ji Minista Maigari Dingyadi.

Sabon Mukaddashin Sufeto Janar Usman Alkali Baba Ya Kama Aiki
Sabon Mukaddashin Sufeto Janar Usman Alkali Baba Ya Kama Aiki

Ya ci gaba da cewa wanna kuma ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya take kokarin yin garambawul da sake fasalin tsarin tsaron kasar, domin samo bakin zaren warware matsalar tsaro da ke addabar kusan dukkan bangarorin kasar.

Shugaba Buhari dai ya bukaci sabon sufeton da ya baiwa marada kunya, ta hanyar tabbatar da nasarar aiwatar da kudurin gwamnati na sake fasalin sha’anin tsaro, da kuma baiwa ‘yan sanda damar gudanar da aikinsu na tabbatar zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa baki daya.

XS
SM
MD
LG