Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Na Bincike Bayan Harin Da Aka Kai a Kusa Da Ofishin Mujallar Charlie Hebdo


Lokacin da Jami'ai suke bincike kan harin wukar na Paris, Satumba 25, 2020. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Lokacin da Jami'ai suke bincike kan harin wukar na Paris, Satumba 25, 2020. REUTERS/Gonzalo Fuentes

Hukumomi a Faransa, sun kaddamar da binciken ta'addanci bayan da wani mahari ya cakawa mutum biyu wuka a kusa da tsohon ofishin mujallar barkwanci ta Charlie Hebdo da ke birnin Paris.

‘Yan sandan na Paris sun ce sun kama mutum biyu, ciki har da wani wanda aka cafke shi a yankin Place de la Bastille da ba shi da nisa da inda aka kai harin.

Da farko hukumomi sun ce mutum hudu ne suka ji rauni a harin, amma daga baya suka ce mutum biyu ne harin ya rutsa da su.

Hukumomin sun ce ba su fayyace ko harin yana da alaka da mujallar ta Charlie Hebdo ba.

Masu ikrarin jihadi sun taba kai hari ofishin mujallar a shekarar 2015 inda mutum 12 suka mutu.

Ana kan yi wa wasu ‘yan ta’adda 14 shari’a kan wannan hari a Paris, bayan da aka tuhume su da hannu a harin.

Ita dai mujallar ta Charlie Hebdo ta fusata Musulmi bayan da ta wallafa wani hoton batanci kan Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam, kuma a baya-bayan nan ma ta sake wallafa wani makamancin wannan hoto na barkwancin gabanin shari’ar da ake yi.

A makon da ya gabata, ‘yan sanda suka dauke shugabar sashen kula da ma’aikatan mujallar daga gidanta bayan da aka yi ta aika mata da sakonnin barazanar kisa gabanin a fara shari’ar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG