Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Hana Jirgin Da Ke Dauke Da Indiyawa 300 Tashi Bisa Zargin Safarar Mutane


Jirgin sama
Jirgin sama

An dakatar da wani jirgin saman da zai nufi kasar Nicaragua dauke da fasinjoji sama da 300 daga kasar Indiya a Faransa bisa zargin “fataucin mutane” a cewar hukumomi a ranar Juma’a.

Jirgin dai ya taso ne daga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa kuma an tsare shi ne bayan samun bayanen sirri.

A yau ranar Juma'a, 22 ga watan Disamba, Ofishin mai gabatar da kara na birnin Paris ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, jirgin da ke dauke da fasinjoji "da alama ya sha fama da safarar mutane."

Hukumar da ke yaki da miyagun laifuka ta kasa JUNALCO ta dauki nauyin gudanar da binciken, kamar yadda masu gabatar da kara suka bayyana.

Ana kyautata zaton cewa 'yan kasar Indiya 303 din suna aiki ne a Hadaddiyar Daular Larabawa.

A cewar wata majiya da ke da labarin lamarin, mai yiwuwa fasinjojin sun yi shirin tafiya Amurka ta tsakiya ne domin yunkurin shiga Amurka ko Kanada ba bisa ka'ida ba.

Fataucin mutane yana da yuwuwar hukuncin daurin shekaru 20 a Faransa.

~AFP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG