A ranar 6 ga watan Maris 1957, Ghana ta sami 'yancin kai, bayan shekaru 83 na mulkin mallaka daga kasar Burtaniya.
Bikin wannan shekarar mai taken: “Hadin kanmu, karfinmu, da manufarmu”, ya samu halartar daruruwan jama’a daga bangarorin kasar daban-daban, jami’an diflomasiyya, malaman addinai, sarakunan gargajiya da masu fada a ji.
Sai dai jam’iyun adawa sun kauracewa bukin bana, domin a cewarsu matsayin da Ghana ke ciki a yau, ba abin da za a yi biki bane.
Shugaban kasa, Nana Akufo-Addo a jawabinsa a wurin bukin, ya tabbatar da cewa lallai kasar na fuskantar kalubale, kuma gwamnatinsa na iya kokarinta wajen magance matsalolin. Ya kara da cewa, kasancewar kasar Ghana ce ta farko da ta samu yancin kai, kudu da hamadar sahara, ta kasance wani ma’auni na ci gaban nahiyar, lallai ya kamata ta kamanta hakan. Ya ce, gwamnatinsa ta kaddamar da wasu matakan kasafin kudi da zai kawo dauki ga kasar.
Bikin samun ‘yancin kai daga mulkin mallaka yana zuwa ne da waiwaye da la’akari da sadaukarwa da aka a tsawon tarihi zuwa yanayin da kasar take a yanzu. Shin tsawon shekaru 66 da Ghana ta samu ‘yancin kai kwalliya ta biya kudin sabulu kuwa?
Pious Ali, asalin dan Ghana ne, kuma a halin yanzu dan majalisar birnin Portland na jihar Maine dake Amurka ya ce, idan Ghana ta samu ci gaba a bangaren dimokradiya, la’akari da shekaru 30 da ta yi tana mulkin dimokradiya babu juyin mulki, sabanin wasu kasashen makwabta.
Haka kuma wasu ‘yan Ghana da Muryar Amurka ta ji ra’ayinsu sun nuna cewa, lallai akwai saura idan aka yi la’akari da arzikin kasar da kuma yanayin kuncin rayuwa da al’ummar kasar ke fama da shi.
Har wa yau a cikin jawabinsa, shugaba Akufo-Addo ya sanar da cewa zai gabatar da jawabi ga majalisar dokoki kan yanayin da kasa ke ciki a ranar Laraba, 8 ga watan Maris kamar yadda sashe na 67 na kundin tsarin mulkin kasa ya gindaya.
Domin Karin bayani ga rahotan Idris Abdullah Bako.