Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Filato Ta Bullo Da Tsarin Sufuri Na Cikin Birni


Gwamna Muftwan yayin da ya ke kaddamar da sabon shirin Tin City Urban Metro Initiative
Gwamna Muftwan yayin da ya ke kaddamar da sabon shirin Tin City Urban Metro Initiative

A cewar sanarwar daya wallafa a shafinsa na x, gwamnan yace tsarin zai saukaka tsadar zirga-zirga a cikin birni tare da kawo sauki ga masu amfani da ababen hawan haya a harkokin sufurinsu na yau da kullum.

A jiya talata Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang ya bullo da tsarin “Tin City Urban Metro Initiative” a turance, inda ya kaddamar da manyan motocin safa 15 kirar MAN-Diesel.

Gwamnan ya kara da cewar, “wadannan motoci sun zarta bas-bas din da muka sani, sun zamo cibiyoyin kirkira masu tafiya, da aka kawata da harkokin sadarwar zamani samfurin NFC da tsarin biyan kudi ta kati.

"Mun shiga wani kadami na zamanantar da tsarin tafiye-tafiyenmu, a bisa dacewa da tsarin da sauran duniya ke tafiya akai na rage amfani da tsabar kudi, domin inganta jin dadin fasinjojinmu”, in ji shi.

Sabin motocin shirin Tin City Urban Metro Initiative
Sabin motocin shirin Tin City Urban Metro Initiative

Ya kara da cewa "kiyaye afkuwar hatsari da sa ido na da matukar mahimmanci a harkar sufurinmu. Kowace bas na dauke da na’urar nadar hoto da sauti domin bada kariya ga fasinjoji tare da bin diddigin yadda ake gudanar da motocin".

Tin City Urban Metro Initiative
Tin City Urban Metro Initiative

A cewar gwamnan, manufar tsarin sufurin shine rage tsadar zirga-zirga a cikin gari tare da saukakawa fasinjoji dawainiyar da suke yi a sufurinsu na yau da kullum.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG