Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Rufe Wuraren Hakar Gwal Mallakin Kasar China


Janar Abdouramane Tchiani
Janar Abdouramane Tchiani

Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne na rufe wuraren hakar ma’adinan zinare dake arewacin kasar bayan da wasu dabbobi suka mutu sakamakon shan ruwa mai dauke da guba a wurin.

Ma'aikatar Kula da Ma'adinan Kasar Nijar ta bada umarnin rufe kamfanin kasar China mai suna Sahara SARL, bayan samun sa da laifin gurbata muhalli da kuma zubar da guba wacce tayi sanadiyyar mutuwar dabbobi da dama.

Hakan ya biyo bayan ziyarar gani da ido, bisa rakiyar jami'an 'yan sanda da ke binciken lamarin, jim kadan bayan ta tabbatar da zargin da makiyayan sukayi na cewa guba na halaka musu dabbobi

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun jima suna kokawa da yadda kanfanonin kasashen waje dake hakar ma’adinai ke gurbata muhalli.

Sulaimane Boube mai fafutukar kare hakkin bil’adama a Agadas ya bayyana gamsuwar sa da wannan matakin

Kungiyoyin dai sun jaddada bukatar tallafin gwamnati ga wadanda abin ya shafa domin taimaka musu maye gurbin dabbobin su da suka mutu

A saurari cikakken rahoton Hamid Mahmoud:

Gwamnatin Nijar Ta Rufe Wuraren Hakar Gwal Mallakin Kasar China
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG