Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Human Right Watch Ta Shawarci Najeriya Kan Boko Haram

Hoton wani gini da ya kone sakamakon hare haren da kungiyar Boko Haram ta kai a Kano.
Hoton wani gini da ya kone sakamakon hare haren da kungiyar Boko Haram ta kai a Kano.

Yau talata kungiyar rajin kare hakkin Bil-Adama ta Human Rights Watch, tayi kira ga gwamnatin najeriya ta kara daukan matakai da zasu kawo karshen hare haren ta’adancin da kungiyar dake da’awar Islama ta Boko Haram ke aikatawa.

Kungiyar mai cibiya anan Amurka tace Boko Haram ce ke da alhakin kashe akalla mutane 935 tund a ta fara kai famaki a 2009, ciki har da mutane 250 a farkon makonnin wan nan shekara. Kungiyar tace galibin hare haren an kaisu ne a cikin jihar Borno ind a kungiyar take da helkwata.

Na baya bayan nan shine hare haren bama-bamai da aka kai ranar jumma data shige da suka halaka akalla mutane 185 a Kano, birni na biyu a girma a Najeriya.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta baci a galibin arewacin Najeriya a kokarin hana aukuwar tashen tashen hankulan.

Duk da haka kungiyar Human Rights watxh tace tilas gwanati ta dauki karin matakai wajen ganin wadanda suke da alhakin kai wadan nan hare hare an gurfanar dasu. Haka kuma tace akwai bukatar a kara yawan ‘yansanda a sassa dake fuskantar tarzomar.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG