Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ‘Yan Majliasar Wakilai Ta Fara Yunkurin Kawo Karshen Tsarin Mulki A Najeriya


Majalisar wakilan Najeriya (Facebook/ Majalisar wakilai)
Majalisar wakilan Najeriya (Facebook/ Majalisar wakilai)

Kungiyar GTA a majalisar wkilai su 60 ta fara wannan yunkurin ne tare da neman a koma tsarin Majalisa da aka yi amfani da a jamhuriya ta farko a Najeriya, saidai wani kwararre da ma wata fitacciyar ‘yar siyasa a Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan wanna yunkurin.

WASHINGTON, D. C. - Kungiyar ‘yan majalisar ta gabatar da wannan kudurin ne a zauren majlisa jiya, Laraba, kuma tuni har an yi wa kudurin karatu na farko, wanda wannan kuduri idan ya samu karbuwa, kungiyar tana so a fara aiki da shi ne a shekara ta 2031.

Daya cikin ya'yan kungiyar kuma wanda ya kawo kudurin a majalisar Abdulsamad Dasuki ya yi karin haske yana cewa wannan tsari shi ne aka yi amfani da shi a zamanin marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.

Dasuki ya ce kungiyar tana ganin shi ne mafita ga kasar a halin yanzu domin tun da aka bar amfani da tsarin zamanin su Sardauna din Najeriya ta zama ba ta da alkibla.

Amma ga kwararre a fanin siyasa da diflomasiyan kasa da kasa kuma malami a Jami'ar Abuja Dr. Farouk Bibi Farouk yana ganin wannan ba shi ne matsalar Najeriya a yanzu ba.

Farouk ya ce akwai tsarin mulki daban-daban da ake tafiyar da su a kasashe dayawa na duniya, alal misali, yadda aka gwamutsa tsari iri biyu a kasar Faransa, akwai Kwaminisanci a kasa irin su Hadaddiyar Daular Larabawa, da kuma irin na shugaba mai cikakken iko, kamar wanda Najeriya ta ke gudanarwa.

Farouk ya ce matsalar a shugabanci ya ke, ya kuma kara da cewa idan an samu irin shugabanci da zai kawo wa kasa ci gaba shi ne abinda zai fi.

To sai dai ftacciyar ‘yar siyasa daga Jihar Kano Hajiya Mariya Ibrahim Baba ta ce tana goyon bayan yunkurin ‘yan majalisa.

Mariya ta ce tsarin shugaba mai cikakken iko yana da matsaloli musamman ma na kashe kudade masu yawa.

'Yar siyasar ta kara da cewa idan har za a iya dawowa da tsarin Firai Minista da na Majalisa tana ganin abin zai yi kyau sosai, saboda za a sa hankali ne a yadda za a kasafta kudade domin ci gaban kasa.

Abin jira a gani shi ne yadda majalisun jihohi za su dauki wannan kudurin idan majalisar kasa ta mika masu kafin a kai ga aiwatar wa.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Kungiyar ‘Yan Majliasar Wakilai Ta Fara Yunkurin Kawo Karshen Tsarin Shugaban Kasa A Najeriya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG