Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda Sun Mamaye Garuruwa A Mali Tare Da Jefa Mutane Cikin Yunwa


MALI
MALI

Wata matsalar jinkai na kara ta'azzara a arewa maso gabashin kasar Mali inda kungiyoyi masu dauke da makamai da ke da alaka da kungiyar IS suka yi wa manyan garuruwan kawanya.

WASHINGTON, D. C. - Lamarin da ya jefa mazauna yankin da suka hada da yara kimanin 80,000 cikin mawuyacin hali na rashin abinci mai gina jiki, kamar yadda mazauna yankin da kuma wata kungiyar agaji suka yi gargadi jiya Laraba.


Garin Ménaka ya shafe watanni hudu ya na killace, lamarin da ya sa kayan abinci tashin gwauron zabi. Sauran kayan masarufi kamar magunguna ma da kyar ake samu, a cewar mazauna wuraren da kungiyoyin agaji.

“Al’amarin na jinkai ya yi muni, inda ‘yan gudun hijira ke bi gida-gida suna neman abinci ga iyalansu. Yara na fuskantar barazanar yunwa,” abin da Wani Ould Hamadi, mataimakin magajin garin Ménaka, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press kenan.

Kasar Mali tare da makwabtanta Burkina Faso da Nijar sun kwashe sama da shekaru 10 su na gwabza fada da kungiyoyi masu dauke da makamai da suka hada da wasu da ke kawance da Al-Qaida da kuma kungiyar IS. Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a daukacin kasashen uku a cikin 'yan shekarun nan, mahukuntan kasar sun kori sojojin Faransa tare da karkata zuwa ga rundunonin sojan haya na Rasha domin neman taimakon tsaro a maimakon haka.

Kanar Assimi Goita wanda ya karbi ragamar mulki a kasar Mali bayan juyin mulkin karo na biyu a shekarar 2021, ya yi alkawarin fatattakar kungiyoyin da ke dauke da makamai, amma Majalisar Dinkin Duniya da wasu manazarta sun ce gwamnatin shi ta yi kasa a gwiwa.

Kungiyar agaji ta Save the Children ta ce kimanin yara 80,000 ne suka makale a cikin garin na Ménaka da ke fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki da cututtuka, kuma da yawa ba sa tare da iyayensu bayan sun tsere daga tashin hankali a wasu wurare.

“Yara a Menaka sun makale cikin wani yanayi mai ban tsoro. Bari mu bayyana a fili; idan ba a cire shingen ba, yunwa da cututtuka za su haifar da mutuwa, ”in ji Siaka Ouattara, daraktan Save the Children na kasar a cikin wata sanarwa.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG