Wannan sabon makari a cewar kwararrun, ya na iya maganin irin nau’in cutar Malari nan da kan bijirewa magani.
Fatan dai shi ne, idan har wannan sabon magani ya yi aiki a jikin bil adama, hakan zai zama wani muhimmin ci gaba da aka samu a kokarin da ake yi a yakin na neman makarin cutar ta zazzabin cizon sauro, musamman ma a fannin samar da rigakafinta,
Kiyasin da aka yi, ya nuna cewa cutar ta Malari na kama mutanen da yawansu ya kai miliyan 200 a duk shekara - a duk fadin duniya.
Farfesa Kelly Chibale, wanda shi ya jagoranci binciken a jami’ar Cape Town dake Afirka ta Kudu, ya ce nau’in sabon maganin wanda suka yi wa lakabi da MMV048, na iya kawo cikas ga matakan da cutar ta zazzabin cizon sauro ke bi wajen yaduwa a cikin magudanun jinin dan dam, ta yadda har zai warkar da cutar cikin wani lokaci.
Cutar zazzabin cizon sauro kamar yadda bincike ya nuna, na sanadin mutuwar mutum dubu 425 a kowace shekara, wadanda mafi yawansu yara ne kanana daga kasashen dake kudu da Sahara a nahiyar Afrika.
Facebook Forum