Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Gabatar Da Kara A Shari'ar Charles Taylor Sun Ce Shaidu Sun Nuna Hannunsa A Cinikin Daiman


Jarumar fina-finan Amurka Mia Farrow tana shirin bayar da shaida a shari'ar Charles Taylor
Jarumar fina-finan Amurka Mia Farrow tana shirin bayar da shaida a shari'ar Charles Taylor

Masu shigar da kara a shari’ar Charles Taylor da ake gudanarwa a birnin Hague sun ce shaidun da aka bayar jiya Litinin sun danganta tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor da cinikin duwatsun daiman

Masu shigar da kara a shari’ar Charles Taylor da ake gudanarwa a birnin Hague sun ce shaidun da aka bayar jiya Litinin sun danganta tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor da cinikin lu’u-lu’u da ake kira “blood diamond” ko kuma lu’u-lu’un haram da aka yi amfani da shi wajen goyon bayan ‘yan tawaye a yakin basasa da suka shafe shekaru goma suna yi, wanda aka kawo karshe cikin shekara ta dubu biyu da biyu. Jiya Litinin, wadansu shaidu guda biyu sun bada shaidu sabanin abinda mai tallar kayan kawar nan ‘yar kasar Birtaniya Na’omi Cambell ta fada. Tsohuwar wakiliyar Cambell Carole White tace Taylor da Cambell sun yi tadi da juna a lokacin liyafar cin abincin, kuma Taylor ya shaidawa mai tallar kayan kawar cewa zai bata lu’u-lu’u. Wata ‘yar wasan fina finai ba’amurkiya Mia Farrow ita ma ta bada shaida jiya litinin cewa ta tuna taga Cambell cike da murna a lokacin da ta fito cin abinci washe gari bayan liyafar, ta kuma gaya mata cewa wadansu mutane sun tashe ta da tsakar dare suka ce Charles Taylor ya aike su suka kuma bata lu’u-lu’u mai girma.

XS
SM
MD
LG