Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matatar Man Fatakwal Zata Koma Bakin Aiki Cikin Watan Afrilu-Kyari


Matatar Mai
Matatar Mai

Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana cewar matatar mai ta Fatakwal zata koma bakin aiki a watan Afrilu mai zuwa.

WASHINGTON DC - Wata sanarwa ta ruwaito Shugaban NNPCL, yana cewar an kammala ayyukan gyare-gyare a matatar wacce ta karbi ganga dubu 450 ta danyen mai ta hanyar tunkudowa daga jerin bututun dake aiki.

Ya kuma kara da cewar, ana daf da kammala ayyukan gyare-gyare a matatun man Kaduna da Warri.

A cewar Mele Kyari, ana sa ran matatar man Kaduna ta fara aiki cikin watan Disamba me zuwa.

Hakan na zuwa ne bayan shekaru 3 da amincewa da kashe dala bilyan 1 da rabi wajen gyara matatar mai ta Fatakwal, daya daga cikin mafi girma a Najeriya.

Matatar man Fatakwal ita ce mafi tsufa a Najeriya, wacce aka gina a 1965, shekaru 9 bayan da aka gano man fetur a karkashin fadamu da dazuzzukan yankin Delta, inda kogin Naija ya koma tekun Guinea.

An gina matatun man Warri dake kusa da Fatakwal data Kaduna dake arewa maso tsakiyar Najeriya a shekarun da suka biyo baya, sa'annan aka ginawa matatar man Fatakwal sabon bangare a shekarar 1989.

Saidai a 'yan shekarun baya-bayan nan rashin aikin matatun yafi aikinsu yawa.

A wani labarin kuma, Majalisar Dattawan Najeriya tayi watsi da rahoton zargin yin almundahana a aikin yiwa matatun man kasar garanbawul da NNPCL ya gudanar.

Duk da kazancewarta kasa mafi arzikin man fetur a nahiyar Afirka, Najeriya ta dogara ne kacokan akan shigo da albarkatun man fetur daga ketare saboda gazawar nata matatun.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG