Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Fuskantar Matsalar Tattalin Arziki


Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.
Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.

‘Yan Najeriya na fuskantar daya daga cikin yanayi mafi muni na tabarbarewar tattalin arziki a kasar ta Yammacin Afirka a cikin shekaru da dama sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Hauhawar farashin ya faru ne sakamakon manufofin kudi da ya sa darajar kudin kasar ya fadi warwas idan aka kwatanta da dalar Amurka. Lamarin dai ya haifar da fushi da zanga-zanga a fadin kasar.

Alkaluman gwamnati na baya-bayan nan da aka fitar a ranar Alhamis, sun nuna hauhawar farashin kayayyaki a watan Janairu ya karu zuwa kashi 29.9 cikin 100, mafi girma tun shekarar 1996, galibi ya shafi abinci da abubuwan sha.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kudin Najeriya, Naira ta kara faduwa inda ake canjin dalar Amurka daya akan Naira 1,524, lamarin da ke nuna asarar da aka samu da kashi 230 cikin 100 daga bara.

“Iyalina yanzu suna rayuwa cikin dogaro ga Allah,” in ji wani dan kasuwa Idris Ahmed, wanda ke da wani kantin sayar da tufafi a Abuja babban birnin Najeriya, kuma cinikinsa ya ragu daga matsakaicin dala 46 a kullum zuwa dala 16.

Faduwar darajar kudin ta kara tsananta a halin da ake ciki na yanzu, kuma yana kara lalata kudaden shiga da kuma na tanadi. Lamarin ya danne miliyoyin ‘yan Najeriya wadanda tuni ke kokawa da wahalhalu saboda sauye-sauyen da gwamnati ta yi ciki har da cire tallafin man fetur wanda ya janyo farashin man ya ninka sau uku.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG