Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Mutuntawa Da Nuna Hakuri Da Juna Ta Duniya


Ranar 16 ga watan Nuwamba rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don karfafa muhimmancin yin hakuri da juna da kuma mutunta juna da ake kira Tolerance Day da turanci.

Farfesa Suleiman Khalil, shugaban tsangayar zamantakewa ta jami’ar Usman Danfodio dake Sokoto yace dukan addinai da al’ummomin duniya, da akidojin jama’a na kokari su karfafa batun hakuri a cikin jama’a, saboda wannan na da muhimmanci a zamantakewar bil’adama.

Ya kuma ce a koda yaushe yana da kyau mutum ya kasance mai hakuri da hali ko yanayin da ya sami kansa, saboda a sami zaman lafiya da kyakkyawan zamantakewa.

Najeriya kasa ce mai addinai, da kabilu, da al’adu da al’ummomi dabam dabam. Farfesa Khalil ya cigaba da cewa hakuri shike rike al’umma, musamman a kasa kamar Najeriya akwai bukatar a karfafa wannan batu. Yawancin lokuta akan sami rikici tsakanin al’umma amma daga karshe hakuri ne kadai zai warware komai.

Ga karin bayani cikin sauti daga Hassan Uamr Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG