Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Aikin Yi Na Barazana Ga Matasa a Afrika


Thomas Waldhauser a jamhuriyar Nijar
Thomas Waldhauser a jamhuriyar Nijar

Rashin abin yi ga matasan Afirka zai ci gaba da zamewa babban barazana ko da kuwa sojoji sun yi nasarar kakkabe yan ta'adar dake nahiyar, in ji Janar Thomas Waldhauser babbab hafsan sojan Amurka dake kula da ayyukan soja a nahiyar Afrika.

A cewarsa, matasa suna da tarin yawa kuma ba su da abin yi in ji Waldhauser.

Da yake wa taron kwamitin ayyukan soja na majilisar dattijan Amurka bayani, Janar Thomas Waldhauser ya ce matsalar tattalin arziki dake zamewa babban kalubale ga matasan nahiyar wata matsala ce kwarai da gaske ga nahiyar.

Ya kuma ce akwai kwarin gwiwar za a samu nasarar a kokarin da ake yi na kakkabe boko haram ko kuma kungiyar ISIL.

Waldhauser ya ce da yawan matasa sun shiga kungiyoyi ‘yan ta'adda ne sabo da ba su da aikin yi, kuma suna neman abinda za su yi domin samun abin zaman gari, ya ce da yawan su ba wai sun yarda da akidojin kungiyoyin ba ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG