Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Amurka Na Gudanar Da Bincike Kan Harin Da Ya Hallaka Fararen Hula 100 A Mosul


Rundunar Sojan Amurka tace tana nan tana duba faifan video daban-daban har 700, wanda aka dauka cikin kwanaki 10 da akayi ana kai hari a Mosul.

Tace makasudin yin hakan shine ta tantance koda gaske ne rahoton nan da ke cewa harin da aka kai ya kashe fararen hula har sama 100, inji mai Magana da yawun rundunar.

Yace “muna kokarin gane gaskiyar wannan batu ne, inji kanar JohnThomas, mai Magana da yawun rundunar sojojin tsakiya ta Amurka, wanda sune ke kula da ayyukan rundunar sojojin Amurka dake aiki a gabas ta tsakiya, yace wannan shine babban abinda yake da muhimmaci a gare mu yanzu game da Mosul”.

Sai dai ma’aikatar tsaron Amurka, wato, PENTAGON, tace kashe fararen hula a arewacin Iraqi, a birnin Mosul, sakamakon wannan harin wani babban abin takaici ne.

Ministan tsaron Amurka, Jim Mattis, ya fada jiya litini cewa ba wata rundunar sojan duniya data nuna damuwar ta akan halin da fararen hula suka shiga, yace sau tari Amurka, tana iya bakin kokarin ta domin ganin an rage hasarar rayukan bayin ALLAH da basu ji ba basu gani ba lokacin duk wani hari da Amurka, keda hannu a ciki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG