Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Rasha Vladimir Putin Yace Tsaurara Takunkumi Akan Koriya Ta Arewa Ba zai Yi Aiki Ba.


Shugaban Amurka da takwaransa na kasar Koriya ta kudu na kiran a kara sanyawa koriya ta arewa takunkumi.

kasashen China da Rasha, dake manyan kawayen Koriya ta arewa, sun ce kiraye-kirayen da ake yi na kara zafafa takunkumi akan Koriya ta arewa bayan gwajin makamin Nukiliyar da ta yi na baya-baya ba zai taimaka ba sosai wajen rage fargaban da ake fama da shi a mashigen koriyoyin biyu.
Da ya ke magana a wajen taron kolin kasashen Brazil, Rasha, da India, da kuma China, na kasashe masu bunkasar tattalin arziki da ake yi a birnin Xiamen na kasar China, shugaban Rasha Vladimir Putin yayi Allah Wadai da gwajin makami mai linzamen da Koriya ta arewa tayi na baya-baya, amma yayi gargadin cewa ruruta wutar daukar matakin soja zai iya haddasa bala’i a duniya.” Putin ya kuma caccaki Amurka akan kiran da ta yi na a kara sanyawa Koriya ta arewa takunkumi “ya kira matakin “mara amfani wanda kuma ba zai yi aiki ba”. Ya kara da cewa shashanci ne Amurka ta sanyawa Rasha takunkumi saboda tana kasuwanci da Koriya ta arewa, kuma daga baya ta dawo tana neman Rasha ta taimaka ta sanya wa yanken da aka maida saniyar ware takunkumi.
Kasashen Rasha da China, da ba sa goyon bayan sanyawa Koriya ta arewa takunkumi, sun roki Amurka da koriya ta kudu kwanan nan, su kawo karshen atisayen sojan da suke yi, don takawa Koriya ta arewa burki akan gwajin makamai masu linzame da na nukiliya da take yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG