Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tankar Mai Ta Kama Da Wuta A Birnin Fatakwal, Ta Halaka Mutane Da Dama - Rahotanni


Wata tankar mai da ta yi gobara a Najeriya (Mun yi aamfani da wannan hoto ne don nuna misali)
Wata tankar mai da ta yi gobara a Najeriya (Mun yi aamfani da wannan hoto ne don nuna misali)

Bayanai sun yi nuni da cewa bayan da tankar ta kama da wuta, ta shafi motoci akalla goma da ke jerin cunkoson ababen hawa a birnin na Fatakwal.

Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu bayan da wata tankar mai ta kama da wuta a hanyar East-West Road a birnin Fatakwal da ke jihar Rivers a kudancin Najeriya.

Jaridun Punch da na Vanguard sun ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:45 na daren Juma’a.

Bayanai sun yi nuni da cewa bayan da tankar ta mai ta kama da wuta, ta shafi motoci akalla goma da ke jerin cunkoson ababen hawa a birnin na Fatakwal.

Wani da ya shaida lamarin ya fadawa jaridar Vanguard cewa ya ji kara har sau biyu masu firgitarwa daga baya kuma hayaki ya turnuke sararin samaniya.

“Idan kuna da ‘yan uwa a Fatakwal ko kira su don ku duba lafiyarsu” Wani mazaunin birnin na Fatakwal mai suna Bassey Esang Don, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba san musabbabin fashewar da ta auku ba ko iya adadin mutanen da suka mutu.

Faduwar tankar mai ta kama da wuta ba bakon abu ba ne a Najeriya, inda a wasu lokuta mutane kan yi rububin zuwa kwasar man idan yana Malala.

Daga nan ne kuma akan samu akasi har wuta ta kama ta lakume rayuwkan mutane.

Wannan al’amari na faruwa ne yayin da farashin mai ya kara tsada a Najeriya inda litar mai ta kusa kai wa Naira 1,000 a sassan kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG