Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sake Sace Mutane 87 A Jihar kaduna


Yan bindiga
Yan bindiga

Akalla mutane 87 ne ‘yan bindiga suka sake sacewa daga muhallansu bayan wata hari da 'yan bindigan suka kai kauyen Kajuru da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

WASHINGTON DC - Hakan ya auku ne a ranar Lahadi, makonni biyu bayan aka yi garkuwa da mutane 14 daga kauyen Dogon Noma, shima a karamar hukumar Kajuru.

Duk da cewar rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna bata tabattar da aukuwar lamarin ba, Shugaban Karamar Hukumar Kajuru, Ibrahim Gajere, ya tabatattar wa tashar talabijin na Channels cewar a misalin karfe tara na daren Lahadi ne ‘yan bindiga suka kai hari kauyen suka yi awon gaba da mazauna kauyen.

Shugaban ya koka da yadda hare-hare suka zama ruwan dare a Kajuru da a halin yanzu ya jefa al’umma cikin zaman dar dar.

A baya bayannan, kananan hukumomin Kajuru da Chikun sun fuskanci hare-hare, ciki har da wanda ya yi sanadin sace dalibai 287 a kauyen Kurigan da ke Karamar hukumar Chikun.

Biyo bayan karuwar sace-sacen mutane a jihar, Babban Hafsan Tsaro na Naeriya, Janar Christpoher Musa ya halarci fadar gwamantin jihar a yau Litinin domin ganawa da Gwamna Uba Sani.

Da yake bayani a yayin ganawan, wanda ya sami halarcin mazauna kauyen Kuriga, Janar Musa ya sha alwashin kubutar da duk dalibai da sauran mutanen da ‘yan bindigan suka yi garkuwa da su.

A cewarsa, jamian tsaro na aiki tukuru domin kwato wayanda ke hannun maharan a yanzu haka.

Ya kuma sha alwashin hukunta duk wadanda ke da hannu a sace-sace da hare-hare a jihar Kaduna da ma sauran jihohin Arewa maso gabas nan ba da jimawa ba.

A makon da ta gabata ne gwamnonin arewacin kasar suka amince da yin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da kuma duba yiyuwar yin amfani da wasu hanyoyin na daban wajen shawo kan karuwar matsalar tabarbarewar tsaro da take addabar yankin arewa.

Sun cimma wannan shawarwar a yayin wani taro da mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya kira tsakaninsa da kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya da manyan hafsoshin tsaro ciki harda Babban Sufeton 'Yan Sanda da kuma kwamandan Rundunar Tsaron Sibil Difens.

An shafe fiye da sa'o'i 4 ana gudanar da taron wanda ya gudana cikin sirri sa'annan bayan kammala shi Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe yayi karin haske game da abubuwan da aka tattauna akai.

Ya kuma bayyana shirin kungiyar gwamnonin ta yin amfani da wasu hanyoyi na daban wajen shawo kan tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG