Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen FARC Na Kasar Colombia Sun Zargi Gwamnati da Shata Karya


Juan Manuel Santos, shugaban kasar Colombia
Juan Manuel Santos, shugaban kasar Colombia

Shugaban kungiyar 'yan tawayen FARC ya zargi gwamnatin Colombia da bayyana abun da yaba cikin yarjejeniyar da suka cimma wada ta daukesu shekaru hudu suna ganawa a kasar Cuba kafin su kaiga daidaitawa

Dakarun kungiyar ‘yantawaye ta F-A-R-C ta kasar Colombia ta zargi gwamnatin kasar Colombia a jiya Lahadi da maimaita karya a sharuddan dake kunshe cikin yarjejeniyar zaman lafiya.

Shugaban 'yan tawayen Rodrigo Londono wanda aka fi sani da lakabin Timochenko yayi gargadin a dandalin twitter cewa, “Sakamakon maimaita karya alkawaurarra da kuma kin bin ka’idojin yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati take, FARC zata bukaci masu sa ido na kasa da kasa” su rinka nazarin yadda ake aiwatarda yarjejeniyar.

Sai dai mai wannan kalamin bai bayyana abinda Londono yake nufi da masu saka ido na kasa da kasa ba, wanda tuni yana cikin tsarin da Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta shata bayanda aka wargaza rundunar mayakan FARC..

Tun kafin a zauna,Shugaban Colombia, Juan (pron: Huan) Manuel Santos yace gwamnati zata tsaya akan shirin da ta tsara na asali. Yace,“Wannan itace matsayar mu kuma zamu cika hakan,” Ya kira yarjejeniyar zaman lafiyar da cewa abu ne da“ba gudu babu ja da baya” gameda ita..

Gwamnati da FARC sun cimma yarjejeniyar bayan sun kwashe shekaru hudu suna daidaitawa a babban birnin Kasar Cuba kafin a watan Nuwambar bara da suka kaiga matsayi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG