Laraba, Disamba 02, 2015 Karfe 07:54

Labarai / Sauran Duniya

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Kudurin Kaucewa Kuncin Kudi

Shugaba Obama ya bayyana shirin da majalisa ta amince da shi a zaman matakin farko a kokarin karfafa tattalin arzikin Amurka.

Shugaba Barack Obama tare da mataimakin shugaba Joe Biden, yana jawabi jim kadan a bayan da majalisa ta amince da kudurin dokar
Shugaba Barack Obama tare da mataimakin shugaba Joe Biden, yana jawabi jim kadan a bayan da majalisa ta amince da kudurin dokar
'Yan majalisar dokokin Amurka sun amince da wani kudurin da zai sa a kauce daga fadawa cikin tarkon nan da ake yi ma lakani da "Tarkon Kuncin Kudi," bayan zartas da wani shirin da shugaba Barack Obama ya bayyana a zaman mataki guda a kokarin karfafa tattalin arzikin Amurka.

Shugaban yayi magana da tsakar daren talata, jim kadan a bayan da majalisar wakilan tarayya wadda 'yan jam'iyyar Republican ke da rinjaye cikinta ta amince da wannan kudurin da tun frko majalisar dattijai ta amince da shi.

Wasu 'yan ra'ayin rikau a cikin majalisar wakilai sun yi kokarin kara zabtare yawan kudaden da gwamnati ta ke kashewa a cikin kudurin, amma kuma ba su samu goyon bayan da zasu iya yin hakan daga sauran 'yan'uwansu a majalisar ba.

Shugaba Obama da 'yan Republican a majalisar dokoki sun shafe fiye da shekara guda su na cacar-baki da juna a kan yawan harajin da za a rika biya, da yawan kudaden da gwamnati zata rika kashewa, da wagegen gibin kasafin kudi, da kuma yadda bashi ke kara yin nauyi a kan gwamnatin Amurka.

Shugabannin majalisar dokokin sun bayyana kudurin da suka zartas da cewa ba shi ne ya fi dacewa ba, amma kuma sun yi shi ne domin kare muradun Amurkawa.

A karkashin shirin da aka zartas din, za a yi karin haraji ma mutum guda mai samun abinda ya zarce dala dubu 400 a shekara, ko mata da miji da suke samun fiye da dala dubu 450 a shekara, matakin da shi ne karin haraji na farko a Amurka a cikin shekaru 20. Har ila yau shirin zai ci gaba da bayar da tallafi na karin shekara guda ga marasa aikin yi tare da kara yawan harajin da ake biya na kudade ko kadarorin gado.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Shrin Safe
  Minti 30

  Shrin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye